Ma’aikatar tsaro ta Kasar Rasha ta wallafa wasu jerin sunayen Sojojin haya da ta kashe wadanda ke taimakawa Ukraine a yakin ta, ciki har da ‘yan Nijeriya 38.
Kamar yadda jaridar Aminiya ta nakalto, Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito cewa ’yan Nijeriya 38 daga cikin 85 da suka je taimaka wa Ukraine, sun mutu, a yayin da 35 suka koma gida, 12 na nan suna ci gaba da yaki a matsayin sojojin haya.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta yi Ikirarin cewa, “Duk da makudan kudin da Kasar Ukraine ke damka wa sojojin hayar, bai hana Sojojin Rasha dandake tarihin sojin hayar ba acikin Duniya.
“Tun daga ranar da Rasha ta afka Ukraine, mutane dubu 1, 831 ne suka isa Kasar Ukraine daga Poland suka zama Sojojin haya da nufin yakar Rasha, inda daga cikin su aka Kashe 378, a yayin da 272 suka arce zuwa kasashensu na asali.
“Akwai sojojin haya 3,321 da ke da rai, wadanda ba a kai ga kama su ba, ko kuma ba a kashe su ba, tana mai cewa daga ranar 17 ga watan Yuni, mayaka ‘yan kasashen waje 1,956 ne Rasha ta kashe, a yayin da sama da 1,700 suka arce zuwa kasashensu.”