Rasha ta zargi Ukraine da kai wa fadar Kremlin hari da jiragen yaki marasa matuka a cikin dare a wani yunkurin kashe shugaba Vladimir Putin da bai yi nasara ba.
Wani babban jami’in fadar shugaban kasar Ukraine ya musanta zargin – wannan shine mafi munin zargi da Moscow ta yi akan fadar Kyiv a cikin watanni 14 da aka yi ana gwabza yaki – kuma ya ce Moscow ta na shirin kai ma kasar Ukraine mummunan harin ta’addanci ne kawai da nufin ramuwar gayya kan zargin da ta yi ma Kyiv.
Fadar Kremlin ta ce Rasha tana da ‘yancin mayar da ramuwa, kuma za a gaggauta ladabtar da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy.
“Jiragen yaki biyu marasa matuki aka datse sun nufi fadar Rasha Kremlin amma sakamakon matakan tsaro da sojoji suka dauka kan lokaci ta hanyar amfani da tsarin na’urar radar, aka katse sadarwar jiragen biyu daga aiki,” in ji Kremlin a cikin wata sanarwa.