Marcus Rashford, ɗan wasan gaba na Manchester United, na gab da kammala komawarsa ƙungiyar FC Barcelona a matsayin aro na tsawon kaka guda. Rashford, mai shekaru 27, ya isa birnin Catalonia na ƙasar Sifaniya a daren Lahadi don kammala sharuɗɗan komawar tasa, bayan samun izini daga Manchester United.
A hotunan da suka karaɗe kafafen sada zumunta, an ga Rashford yana sauka daga jirgin sama a Barcelona. Tattaunawa tsakanin Barcelona da Manchester United ta yi nisa tun makon da ya gabata, kuma a ƙarshe, an cimma yarjejeniya a ƙarshen makon.
- Manchester United Da Everton Na Zawarcin Wilfred Ndidi
- Rashford Na Fatan Buga Ƙwallo Tare Da Lamine Yamal A Barcelona
Yarjejeniyar zata ba wa Rashford damar zama a kulob ɗin na tsawon watanni goma sha biyu (12), tare da zaɓin sayensa dindindin idan ya nuna bajinta. A baya, Rashford ya bayyana sha’awar zuwa Barcelona tun watan Disamba, yana mai cewa yana buƙatar sabon ƙalubale, musamman bayan sabon kocin United, Ruben Amorim, ya nuna ba ya buƙatarsa.
Idan komawar ta tabbata, wannan zai kasance karo na biyu da Rashford ke tafiya aro, bayan ya yi wani aro na watanni shida a kulob ɗin Aston Villa a kakar da ta gabata. Ana sa ran zai kammala gwajin lafiyarsa a farkon wannan mako.
Barcelona na fatan Rashford zai samu damar shiga cikin tawagar da za ta yi wasannin rangadi a Japan da Koriya ta Kudu daga ranar Alhamis mai zuwa, domin fara sabuwar kakar da kyakkyawan shiri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp