Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ko shakka babu yana tafiyar da harkokin mulkin yan Nijeriya yadda yake ganin ya yi ma shi dai dai, idan aka kalli karamin kasafin kudin na Naira Tiriliyan 2 da bilyan176 wanda ya sa ma hannu ranar Laraba ta makon da ya gabata, saboda wasu abubuwan da dole bane sai an yi su musamman ma idan aka yi laakari da yadda ake fuskantar matsalar tattalin arziki wanda ya tabarbare. Id Idan aka duba maganar dala milyan 38 saboda jiragen Shugaban kasa, dala milyan 6.1 na motocin alfarma da wasu milyoyin dala na gyare- gyare,maganar abincin Shugaban kasa,da motocin alfarma na ofishin matar Shugaban kasa na kasar waje da kuma bukatun wasu yanmajalisa da dai sauransu.
Yanzu yana son jamioi wadanda su ke tafiyar da rayuwarsu da kyar cikin matsi saboda rashin kudi yana bukatar su rika ba shi kashi 40 na kudaden shigar da suke samu zuwa lalitar gwamnatin tarayya, saboda samun damar aiwatar da wadansu bukatu na Shugaban kasa wanda bayan ya ji bai yadda da maganar ban amince ba har sai da wani ya kira ni ya yi mani bayani kan alamarin.
- Hadarin Mota: NIS Ta Tabbatar Da Mutuwar Jamianta 4, 7 Sun Ji Rauni A Kano
- Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Ngaski Ya Samu ‘Yanci Bayan Shafe Makonni 3 A Hannun ‘Yan Bindiga
Jaridar LEADERSHIP ta ba da rahoton cewa wannan makon da ake ciki babbar Akanta ta kasa Mrs Oluwatoyin Madein ta aika da takarda ga dukkan jamioin gwamnatin tarayya mai taken Fara aiki da cire kashi 40 kai tsaye na kudaden shigar manyan makarantun da gwamnatin tarayya ke basu wani kaso.”
Daraktan kudaden shiga da zuba jari a ofishin babban akanta na kasa Felid Ore-ofe Ogundairo, shi ne ya ce, An umarce ni cewa Ministan kudi da Ministan tattalin arziki sun amince da fara amfani da cire kashi 40 na kudaden shigar da manyan makarantun da gwamnatin tarayya ke daukar dawainiyar wasu daga cikin bukatunsu, kamar yadda tanaje- tanajen sashe na 62 na dokar data shafi kudi ta shekarar 2020 daga watan Nuwamba 2023.