Mai shari’a Chizoba Orji na wata babbar kotu da ke Abuja, ya gurfanar da shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, Abdulrasheed Bawa, da laifin kin biyayya ga kotu dangane da gazawar hukumarsa na kin bin umarnin da kotun ta bai wa Hukumar.
A hukuncin da kotun ta yanke, kotun ta ce “Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti ya yi watsi da umarnin wannan kotu mai girma da ta bayar a ranar 21 ga watan Nuwamba 2018 wanda ta umurci Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annuti da ta mayar da wata mota kirar Range Rover da kuma adadin kudi Naira N40, 000,000 da ta kwace.
“Bayan ya ci gaba da bijirewa umarnin kotun da gangan, ya cancanci a daure shi a gidan yari na Kuje saboda rashin biyayyarsa na ci gaba da bijirewa umarnin kotun da ta bayar a ranar 21 ga watan Nuwamba, 2018, har sai ya nemi afuwar kotun sannan kuma ya san darajar ta.
“Babban sufeto na ‘yan sanda ya tabbatar da cewa an aiwatar da umarnin wannan kotun mai girma nan take,” in ji alkalin.
Mai shari’a Orji ya ki amincewa da hujjojin da lauyan EFCC ya gabatar mata, Francis Jirbo, domin kare shugaban sa kan matakin da yasa shugaban nasa bai bi umurnin kotun ba.
An yanke hukuncin ne a kan wani kudiri mai lamba FCT/HC/M/52/2021 da Air Vice Marshal (AVM) Rufus Adeniyi Ojuawo ya shigar, wanda ya taba zama Daraktan Ayyuka a Rundunar Sojojin Sama (NAF).