Akwai fargabar kungiyar malaman jami’o’in Nijeriya ASUU na gangamin shiga wani sabon yajin aiki saboda mastalolin da suka hada da rashin cika alkawarin da gwamnati ta yi musu kafin suka janye yajin aikin da suka shiga a lokuttan baya da kumja rashin mutunta dukkan yarjejeniya da amince stakaninsu da gwamnati. Bukatun nasu sun hada da karin albashi da alawus alawus.
Haka kuma malaman jami’an sun nuna rashin jin dadinsu a kan yadda Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ki sake musu albashin wata 8 da suke bin gwamnati sakamakon yajin aikin da suka shiga a shekarar 2022 da kuma alkarin karin naira 35,000 a albashin malaman.
- Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Fitar Da Hatsi Ton Dubu 42 Don Rage Tsadar Abinci A Nijeriya
- Yadda Nijeriya Ta Taka Rawar Gani Har Zuwa Zagayen Karshe Na Gasar AFCON
Kungiyar ASSU ta kuma ce, gwamnatin tarayya ta kasa cika dukkan alkawuran da ta yi wa kungiyar da ma alkawarin da ta yi wa dukkan kungiyouin kwadago na kasar nan tun da ya zama shugaban kasa.
Bincike ya nuna cewa, wannan gwamnatin ba ta yi wani abin a zo a gani ba wajen biyan bukatun kungiyar ASSU duk kuwa da alkawarin da shugaba Tinubu ya yi na tabbatar da ASSU basu sake shiga wani yajin aiki ba a nan gaba.
Shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa, gwamnati ba ta aiwatar da yarjejeniyar da ta cimma ba da kungiyoyin kwadago ba musamman ASSU tun da shugaba Tinubu ya hau karagar mulki.
Ya kuma ce, a halin yanzu kungiyar na tuntubar rassan ta don neman ra’ayin mambobi domin sanin matakin da aza su dauka a karshen wannan watan.