• English
  • Business News
Friday, July 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Halartar Gwamnoni Taron Yi Wa Tsarin Mulki Kwaskwarima A Kaduna Ya Haifar Da Cece-kuce

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
3 hours ago
in Labarai
0
Rashin Halartar Gwamnoni Taron Yi Wa Tsarin Mulki Kwaskwarima A Kaduna Ya Haifar Da Cece-kuce
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram
  • Sauya Tsarin Mulki Ya Kamata A Yi Ba Wai Gyarawa Ba – Shugaban Kwamitin
  • Abin Takaici Babu Gwamnoni A Wurin Taron – Aisha Isma’il
  • Kano Tana Bukatar Karin Kananan Hukumomi 26 Da Samar Da ‘ Yansandan Jihohi – Gwamnatin Kano

 

Batun yi wa kundin tsarin mulkin Nijeriya gyaran fuska abu ne da har yanzu ke jan hankali a kasar nan, musamman a yankin Arewacin. Inda galibin masu tsokaci na ganin lokaci ya yi na yin gwaskwarima ga kundin musamman a bangaren rabon kudadan albarkatun kasar da wasu bangarori da dama.

A wani taron jin ra’ayin alummar yankin Arewa maso yamma wanda kwamitin majalisar wakilai kan gyaran kudin tsarin mulkin Nijeriya suka shirya a Jihar Kaduna, a kasarin wadanda suka tafka muhawara da bayar da bahasi a zaman da kwamitin majalisar ta shirya na kwana daya na son ganin an aiwatar da sauye-sauye a kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekara 1999.

A zantawarsa da wakilinmu jim kadan bayan Kammala taron, shugaban kwamitin sauya kundin tsarin mulki na shiyyar Arewa maso yamma, Honarabul Madaki Aliyu Sani, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban marasa rinji na majalisar wakilai, ya bayyana cewa sauya tsarin mulki ya kamata a yi ba wai kawai gyarawa ba.

Ya jaddada cewa kwamitin da yake jagoranta yana duba kudirori 18 da suka shafi fannoni 13, ciki har da sauye-sauyen harkokin zabe, gyaran bangaren shari’a, karfafa ayyukan majalisa, tsaron kasa da kafa ‘yansandan jihohi, mulki mai amfanar da kowa, rabon kudade, hakkin Dan’adam, ‘yancin kananan hukumomi, kirkirar sabbin jihohi da kananan hukumomi, matsayin sarakunan gargajiya, kasa da ‘yan kasa, cigaban matasa da mata.

Labarai Masu Nasaba

Nazari Game Da Rayuwar Muhammadu Buhari

Sojoji Sun Daƙile Wani Harin Ta’addanci Tare Da Cafke Wasu Mutum Biyu A Taraba

Ya kuma kara da cewa tsarin zai bai wa dukkan ‘yan Nijeriya dama su bayar da gudummawarsu daga dalibai, shugabannin gargajiya, kungiyoyin fararen hula, mata da matasa.

Daga cikin manyan batutuwan da zaman ya mayar da hankali a kansu akwai maganar kirkiro sababbin jihohi da samar da ‘yansandan jihohi da sakar wa kananan hukumomi da bangaren shari`a mara, sannan akwai batun bai wa sarakunan gargajiya ‘yancin kansu.

Sai dai mahalarta taron sun fi mayar da hankali wajen gabatar da kudirin kirkiro sabbin jihohi da samar da ‘yansandar jihohi duk da cewa akwai bangarori da dama da kwamitin zai yi gyara a kai, amma ba su tabo ba.

Jihohin da aka yi wannan zama sun hada da Jihar Kaduna da Kano da Katsina da kuma Jigawa, wadanda wakilai daga jihohin da kungiyoyin farar hula suka gabata da kudirorinsu a gaban kwamitin.

Rashin halartar gwamnonin jihohin guda hudu ya haifar fa cece-kuce a yayin zaman jin ra’ayoyin al’umma duk da cewa jihohin Kaduna da Kano sun samu wakilcin mataimakansu.

Da yawan mahalarta taron sun bayyana shakkunsu kan taron jin ra’ayoyin al’umma, inda wasu suke ganin lamarin akwai lauje cikin nadi, yayin da wasu suka ke ganin yanzu ba lokacin jin ra’ayoyin al’umma ba ne kan gyaran kundin tsarin mulki, lokaci ne da gwamnati ya kamata ta samar da abubuwan inganta rayuwarsu.

Da yake gabatar da kudirin al’ummar Jihar Kano, mataimakin gwamnan, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya ce ganin yadda Jihar Kano take kara tumbatsa da mutane, hakan ya sanya suke bukatar a kara musu yawan kananan hukumomi guda 26 kan wadanda suke da shi guda 44, a jimlace Jihar Kano tana bukatar kananan hukumomi guda 70 da kuma kirkiro musu sabuwar jiha guda daya.

Ya ce gwamnatin Jihar Kano tare da daukacin al’ummar jihar suna goyon bayan kirkiro ‘yansandan jihohi tare da sake fasalin yadda ake raba kason kudadan albarkatun kasar. Ya ce akwai wasu jihohin da suke neman karin abin da suke samu wanda Jihar Kano tana daga cikinsu.

Mataimakin gwamnan ya kuma ce ya, “Ya kamata mu tantance irin yadda ya kamata tsaron kasarmu ya kasance da ci gabanta da kuma ci gaban al’ummarmu, saboda haka ne ma ya sa muke goyon bayan a kirkiro da ‘yansandar jihohi.”

Tsohuwar ministan ma’aikatar mata, Hajiya Aisha Isma’il ta bayyana takaicinta ne bisa rashin halartar gwamnonin Arewa da ministoci wurin taron. Ta ce a jihohin kudancin kasar nan lamarin ba haka yake ba.

“Dan Allah ka duba ka gani taro mai muhimmacin irin wannan amma abin takaici babu gwamna ko daya da ya zo wurin taro, ya kamata a ce duk abin da za a yi muhawara kansa suna ji suna gani domin da zarar an bar nan duk abin da aka tattara da shi za su koma a tantance.

“Haka aka yi a lokutan baya sa’ilin rabon albarkatun man fetur, gwamnonin suka yi ko-in-kula, sai daga baya abin ya damesu. Gaskiya rashin halartar gwamnonin Arewa wurin wannan taron koma baya ne matuka.”

Da take gabatar da kudirinta a gaba kwamitin, tsohuwar ministan ta ce ya zama wajibi a rika bai wa mata kashi 80 cikin dari ne na mukaman siyasa da kujerun majalisun tarayya ba wai kullum a ce mata za a samar musu da kashi 35 cikin dari ba.

Ta bukaci kwamitin majalisar wakilai kan gyaran kudin tsarin mulkin Nijeriya da su tabbatar da cewa sun yi amfani da rahotannin da suka karba daga wurin al’umma masu muhimmaci wajen gyaran kundin tsarin kasar.

Tana mai cewa,”Ka ga akalla akwai sashi kamar guda 75 da ake son a gyara a cikin kudin tsarin mulkin Nijeriya, saboda haka ya kamata a sanya abubuwan da za su amfani al’ummar yankin Arewa da yawa maimakon sanya abubuwan da za su cutar da al’ummar,” in ji ta.

Da take gabatar da kudirin al’ummar Jihar Katsina, Kwamishiniyar Shari’a ta jihar, Barista Fadila Dikko ta yaba wa majalisar tarayya bisa shirya wannan taro, tare da jaddada cewa gwamnatin Jihar Katsina za ta ci gaba da ba da gudummawa don ganin an samar da tsarin mulki da ya dace da kowa, ya kunshi gaskiya, adalci, zaman lafiya da ci gaban Nijeriya.

Barista Fadila ta gabatar da shawarwari masu zurfi da nuni ga bukatar sauya kundin tsarin mulkin kasar nan domin inganta dimokuradiyya, samar da shugabanci mai tafiya da kowa da kowa, da kuma bai wa jihohi da kananan hukumomi cikakken ‘yancin gudanar da harkokinsu.

A cewarta, abubuwan da jihar Katsina ta mayar da hankali a kansu sun hada da rage cunkuson iko daga gwamnatin tarayya da kuma bai wa jihohi da kananan hukumomi cikakken iko a fannonin gudanar da rayuwa. Jihar ta ba da sabon tsarin rabon kudade kamar haka:

 

Gwamnatin Tarayya: daga kashi 52 zuwa kashi 37

Jihohi: daga kashi 36.72 zuwa kashi 31

Kananan Hukumomi: daga kashi 20.60 zuwa kashi 32

Ta kuma bukaci tsarin haraji da zai kasance mai adalci da dai-daito bisa la’akari da albashi da gudunmawar tattalin arziki.

Hazakika, ta ce akwai bukatar gyaran zabe da mulkin kananan hukumomi, inda ta bukaci a kafa hukumar zaben kananan hukumomi mai zaman kanta, a tabbatar da sahihancin zabe da warware gardama kafin rantsar da sabbin shugabanni da kuma daidaita kudin yakin neman zabe.

Jihohin Kaduna da Jigawa duk sun mayar da hankali ne wajen goyon bayan samar da ‘yansandar jihohi’ da kirkiro sabbin jihohi.

Da yake magana a madadin Majalisar Sarakunan Gargajiya, Sarkin Zazzau Ambasada Nuhu Bamalli ya ce babu abin da sarakunan gargajiya suke bukatar illa a ba su ‘yancin kansu ta hanyar samar musu da hukumar da za ta rinka sanya ido kan batun sarakunan gargajiya wanda za ta yi aiki babu katsalandan.

Ya ce wannan taron an yi shi a daidai lokacin da sarakunan gargajiya suke bukatarsa.

Shi ma Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta kasa (NBA) reshen Jihar Kano, Barista Usman Umar Fari ya ce, “Mun gabatar da abubuwan guda hudu da suka shafi yawaitar muyagun kwayoyi a Nijeriya, akwai mutum miliyan goma sha hudu da suke tu’ammali da muyagun kwayoyi, wanda ya kamata a yi gyara kan yawaitar muyagun kwayoyi.

“Haka kuma muna so a gyara sashi na 197 karamin sashi na (1) domin ya kafa hukumomi lura da muyagun kwayoyi na jihohi don a hada karfi da karfe a yaki wannan muyagun kwayoyi domin hukumar yaki da muyagun kwayoyi ta kasa ita kadai ba za ta iya yakar wannan matsalar ba.”

Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi (NULGE) na shiyyar Arewa maso yamma, Kwamared Abdullahi Muhammad Gwarzo, ya jadada bukatunsu ga kwamitin da a sakar wa kananan hukumomi mara duk da cewa kotun koli ta yanke hukuncin bai wa kananan hukumomi ‘yancin kansu amma har yanzu babu labari.

Sai dai yayin da wasu ke maraba da wasu batutuwan da aka gabatar, akwai masu adawa da shi ganin cewa yanzu ba lokaci ba ne na neman sauyi a kundin la’akari da wasu tarin batutuwan da ke addabar kasa kamar yadda wasu kungiyar mata da suka halarci zaman suka gabatar.

Sun bayyana cewa kamata ya yi a ce gwamnati ta mayar da hankali wurin kawo saukin tsadar rayuwa da matsalar rashin tsaro da ya addabi yankin Arewa, amma an yi watsi da su an mayar da hankali kan abin da ba zai amfanir talakawa ba.

Madam Sara Manya da Malama Hannatu Musa sun shiada wa wakilinmu cewa ba sa goyon bayan wannan taron, musamman ganin wannan shi ne karo na uku ana yin irinsa a Kaduna amma da zarar an fara sai a ce lokacin zabe ya yi sai bayan an kafa wata gwamnatin sai kuma a faro daga farko.

Sun ce lokaci ya yi da gwamnatocin kasar nan za su sauke nauyin da al’umma suka dora musu yayin yakin neman zabe, wanda hakan shi ne zai taimaka musu, amma ba wai gyaran kundin tsarin mulkin kasar ba.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Tinubu Ya Kammala Hanyoyi 420 A Sassan Nijeriya Cikin Shekara 2

Next Post

Kaduna: An Horar Da Sarakunan Gargajiya Kan Sasanta Rikici Da Samar Da Zaman Lafiya

Related

Nazari Game Da Rayuwar Muhammadu Buhari
Labarai

Nazari Game Da Rayuwar Muhammadu Buhari

24 minutes ago
Sojoji Sun Daƙile Wani Harin Ta’addanci Tare Da Cafke Wasu Mutum Biyu A Taraba
Manyan Labarai

Sojoji Sun Daƙile Wani Harin Ta’addanci Tare Da Cafke Wasu Mutum Biyu A Taraba

2 hours ago
'Yan Bindiga
Labarai

Kaduna: An Horar Da Sarakunan Gargajiya Kan Sasanta Rikici Da Samar Da Zaman Lafiya

2 hours ago
yola
Labarai

Tinubu Ya Kammala Hanyoyi 420 A Sassan Nijeriya Cikin Shekara 2

4 hours ago
Gwamnan Zamfara Ya Tallafa Wa Yara Mata 8,225 Da Ke Sakandare
Labarai

Gwamnan Zamfara Ya Tallafa Wa Yara Mata 8,225 Da Ke Sakandare

5 hours ago
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Manyan Jami’an ‘Yansanda 150 Ke Fuskantar Kwamitin Ladabtarwa

6 hours ago
Next Post
'Yan Bindiga

Kaduna: An Horar Da Sarakunan Gargajiya Kan Sasanta Rikici Da Samar Da Zaman Lafiya

LABARAI MASU NASABA

Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)

Akwai Bukatar Daina Cin Zarafin Malaman Makaranta

July 18, 2025
Nazari Game Da Rayuwar Muhammadu Buhari

Nazari Game Da Rayuwar Muhammadu Buhari

July 18, 2025
Wata Motar Tankar Mai Ta Kama Da Wuta Tare Da Kone Wasu Motoci A Ibadan, Jihar Oyo

Wata Motar Tankar Mai Ta Kama Da Wuta Tare Da Kone Wasu Motoci A Ibadan, Jihar Oyo

July 18, 2025
Sojoji Sun Daƙile Wani Harin Ta’addanci Tare Da Cafke Wasu Mutum Biyu A Taraba

Sojoji Sun Daƙile Wani Harin Ta’addanci Tare Da Cafke Wasu Mutum Biyu A Taraba

July 18, 2025
'Yan Bindiga

Kaduna: An Horar Da Sarakunan Gargajiya Kan Sasanta Rikici Da Samar Da Zaman Lafiya

July 18, 2025
Rashin Halartar Gwamnoni Taron Yi Wa Tsarin Mulki Kwaskwarima A Kaduna Ya Haifar Da Cece-kuce

Rashin Halartar Gwamnoni Taron Yi Wa Tsarin Mulki Kwaskwarima A Kaduna Ya Haifar Da Cece-kuce

July 18, 2025
yola

Tinubu Ya Kammala Hanyoyi 420 A Sassan Nijeriya Cikin Shekara 2

July 18, 2025
Gwamnan Zamfara Ya Tallafa Wa Yara Mata 8,225 Da Ke Sakandare

Gwamnan Zamfara Ya Tallafa Wa Yara Mata 8,225 Da Ke Sakandare

July 18, 2025
Manzon Allah

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447 Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (3)

July 18, 2025
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Manyan Jami’an ‘Yansanda 150 Ke Fuskantar Kwamitin Ladabtarwa

July 18, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.