Sauran abubuwan da suke taimakawa kamar yadda ya yi bayani masu matukar muhimmanci sune mutane masu zaman kansu, hukumomi,sai kuma ga shi basu taimakawa kokarin da gwamanati kamar yadda ya dace, saboda ita kadai ba zata iya tafiyar da lamarin ilimi ba.
Ya yi kira da abokan tafiya na kasa da kasa da sauran masu zaman kansu su taimakawa gwamnati ta wajen daukar nauyin masu taimakawa,cigaba da aiki dasu,da irin aibashin da za a rika ba masu taimakawar.
- Masu Zanga-zanga Sun Fito Duk Da Dokar Hana Fita A Jigawa
- Zanga-Zanga Ta Yi Sanadin Ɓarna Mai Yawa A Jigawa, An Sanya Dokar Hana Fita
Saboda yawancinsu duk malaman makaranta ne,suna bangare na ilimi.Hakanan ma yawancin gwamnatocin Jihohi basu maida hankalinsu ba wajen daukar aiki na masu taimakawa da kuma ci gaba da tafiya tare.Shi yasa duk yadda aka kalli lamarin yaki da jahilci bada gaske ake ba,musamman ma idan aka dubi yadda kowa zai iya taimakawa.
Masanin ilimi, Micheal Ojonugwa, cewa ya yi babbar matsalar da ake fuskanta wajen kokarin da ake da yaki da jahilci shine yawan wadanda basu da ilimi matsalar yaran da basu zuwa makaranta a Nijeriya.
Ya jaddada idan har ana da matasa da manya masu yawa da suke da ilimi su da kansu za suyi kokarin ganin sai ‘ya’yansu ko ‘yan’uwansu sai sun sa su makaranta,da haka ne kuma kokarin nasu zai rage yawan yara wadanda basu zuwa makaranta.
Akwai dalilai masu yawa wadanda suka kasance wani tarnaki akan yawan wadanda basu da ilimi,babba daga cikinsu shine yawancin iyaye suna fama da talauci, lamarinsu bai wuce abinda za su ci ba,babu wata maganar zuwa makaranta.
Ojonugwa kamar yadda ya kara jaddadawa matsalar da tafim cimma al’umma tuwo a kwarya al’umma ita ce matsalar tsaron da ake f ama da a Nijeriya, inda dalibai da malamai a makaranta ake masu Kallon wadndaza a iya daukewa ayi garkuwa dasu har ma da kashewa. Wannan shi yake sa was uke cewa yafi dacewa su tsaya gida maimakon a dauke su da sunan neman ilimi.
Kamar yadda yace: “fifikon da ake da shi tsakanin tsakanin wannan sashen da wancan da akwai bukatar a dauki mataki cikin gaggawa a wuraren da karanci wadanda suka yaki jahilci.Maganar gaskiya idan har za a samu damar kara yawan masu ilimi sannu a hankali lamarin rashin tsaro watarana zai zama tarihi,saboda yawancin wadanda ake amfani dasu basu da ilimi ne da kuma muaten da suke ganin an maida su saniyar ware.”
Yayin da yake cewa lamarin mizanin masu ilimi ya kamata ace an wuce inda ake a yanzu kamar yadda ya ce ‘’ amma kuma Nijeriya tana fama da matsalar rashin tsaro, fatara,da sauran matsaloli, abin so ne aga cewar an yi maganin matsalolin kafin a samu wani cigaba kan lamarin da ya shafi karuwar masu mizanin masu ilimi.”
Wani jami’ar ilimi wadda take kulawa da lamarin daya shafi yaki da jahilci a wasu cibiyoyi na Abuja amma bata son a ambaci sunanta,tace yawancin cibiyoyi ba masu zuwa da yawa, domin su yaki jahilci,saboda ba a wayar da mutane ba, basu san abinda ake ba, basu sanin muhimmancin mutumin da ya kasance mai ilimi ba.
Ta ce yawancin manya yanzu suna maida hankali ne a lamarin kasuwanci da wasu ayyukan da basu taka nkara sun karya ba, maimakon zuwa makaranta.
“Amma kuma ba za a ga laifinsu ba saboda fatara ko talauci suna damuwar kowa a Nijeriya, ya kuma kamata mutane su ci abinci tukuna kafin su dauki mataki kan wani abinda suke son yi kamar yadda dace,”.
Gwamnatoci na daban- dabn ya dace su zuba jari sosai a bangaren ilimin yaki da jahilci idan har ana son samun cigaban ilimi a Nijeriya, yayin da take ga masu hannu da shuni su taimaka wajen kara bunkasa sashen domin ya bunkasa.