Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ba ta da mafita ga dukkan matsalolin da suke addabar kasar nan ba, amma duk da haka ba za a dora mata laifin rashin kokari da maida hankali wajen ganin ta daidaito da lamura ba.
Ya shaida hakan ne a lokacin da ke ganawa da wasu gwamnonin Nijeriya da wasu zababbun masu kamfanonin a fadarsa da ke Abuja.
- Gwamnatin Buhari Ita Ce Mafi Muni A Tarihin Nijeriya – Mahdi Shehu
- Shirin Gwamnati Na Samar Da Mafi Karancin Albashi
Daga cikin wadnada suka halarci zaman har da gwamnoni, Charles Soludo (Anambra) da Dapo Abiodun (Ogun); Aliko Dangote, Abdul Samad Rabiu, Tony Elumelu, da Mista Segun Ajayi-Kadir darakta janar kungiya hada kayayyaki a Nijeriya (MAN).
Hadakar an maida ita yanzu ta zama kwamitin da zai bai wa shugaban kasa shawarorin yadda za a farfado da tattalin arzikin Nijeriya da ke cikin halin-ni’yasu.
Tinubu ya lura kan cewa akwai bukatar a kara azama da sanya abubuwa kan turbar da suka dace domin ganin an sake dawo da tattalin arziki cikin hayyacinsa.
A cewarsa, gwamnatinsa za ta sake bullo da wasu tunani da ra’ayoyin da za su kai ga taimaka wa talakawa da fitar da su daga matsalolin tattalin arziki, yana mai ba da tabbacin cewa abubuwa za su daidaita kuma tattalin arziki zai farfado.
Tinubu ya kara da cewa, “Yana da kyau mu zauna mu duba mene ne muke yinsu daidai mene ne kuma ba ma yi daidai domin ganin mun dawo da tattalin arziki cikin hayyacinsa. Kamar yadda na sha fada ne a baya, al’ummar kasar nan sun cancanci mu faranta musu rai matuka gaya. Kuma, tabbas babu shakka mun damu sosai da halin da dalibai da iyaye mata zuwa iyaye maza ke ciki, mun damu da manoma, ‘yan kasuwa da kowa da kowa wajen ganin mun tabbatar an samu sauki cikin lamura.”