Tsohowar ministar ilimi, Dakta Obiageli Ezekwesili ta bayyana cewa rashin ingantaccen shugabancin siyasa ne silar wahalhalun tattalin arzikin da ake fama da su a Nijeriya.
Ezekwesili ta bayyana hakan ne wajen wani taro, inda ta yi kira a yi kokarin sauya tsarin mulki da siyasa da tsarin zabe da kuma tattalin arzikin kasar nan.
- An Nuna Dandanon Shirye-Shiryen Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Na CMG A Filin Jiragen Sama Da Yankunan Kasuwanci Na Dubai
- Ina Da Labarin Sirri ‘Yan Bindiga Za su Kawo Mun Farmaki – Gwamna Dikko Raɗɗa
Ta ce idan ana bukatar ci gaba dole ne ‘yan Nijeriya da sauren kasashen Afirka su sami ingantacciyar shugabancin siyasa.
Ezekwesili ta bayyana wa mahalarta taron cewa gazawar kasa ya ta’allaka ne ga irin shugabancin ko yadda ake mulkar mutane da kuma yadda ake tafiyar da albarkatun kasa ba ta hanyar kashin kai ba sai dai ta yadda zai inganta rayuwar al’umma.
Ta lallai idan ba a dauki wasu matakai ba a Nijeriya babu abin da zai iya sauyawa ko nan da shekaru 2060 ne, dole ne a gyara yaddda ake gudanar da shugabancin siyasa a kasar nan. A cewarta, ‘yan siyasar kasashen Afirka ba sa iya gudanar da tsarkakken shugabancin tsakanin su da mutane.
A kan haka ne, Ezekwesili ta yi kira da a samar da sabuwar kungiya da za ta iya mamaye fagen siyasar Nijeriya da za ta hada masu kima da ka iya sauya alkiblar siyasar Nijeriya.
Ta kara da cewa akwai bukatar samar da sabon tsari ta hanyar horar da ‘yan Nijeriya a bangaren siyasa da kuma tsare-tsarin harkokin mulki ga wadanda aka bai wa sabbin mukamai domin sanin makaman aiki da za su kadada wa al’ummar da suke mulka. Sannan ta ce akwai bukatar ‘yan Nijeriya su hada kai tare da yin aiki kafada da kafada domin samun damar kyara kundin tsarin mulki da siyasa da harkokin zabe da kuma habaka tattalin arzin kasar nan.
“’Yan Nijeriya ne kawai za su iya aiki kafada da kafada domin tilasta wa bangarorin gwamnati uku tare da mayar da martanin gaggawa wajen dakile durkushewar kasar nan. Nijeriya ce kasa ta 13 a jerin kasashen duniya da suka gaza,” in ji ta.
A nasa bangaren, Farfesa a Jami’ar Stanford da ke kasar Amurka, Larry Diamond ya yi Allah wadai da yadda jam’iyyar mai mulki ke mamaye siyasar kasa da harkokin zabe har ya hana gudanar da sahihin zabe a kasa.