Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Taskira, shafin da ke fita a kowanne mako cikin wannan Jarida ta Leadership Hausa.
Hakika muna ganin sakonninku kuma muna godiya bisa addu’o’inku gare mu.
Tsokacin yau zai yi duba ne game da matsalar da ke addabar wasu mutanen, matsalar da ta kewaye mafi yawan gidajen al’umma, wadda a yanzu za a iya kiranta da ruwan dare – game duniya ta bakin masu iya magana.
Ba komai bace face matsalar rashin jituwa a tsakanin ‘yan’uwa na jini, wanda suke uwa daya uba daya ko kuma wanda suka hada uba daya ko wanda aka hada uwa daya ba uba daya ba, da makamancin haka.
Da yawan gidaje ana samun irin wannan matsalar, wanda kuma wasu kan rasa gane musabbabin afkuwar hakan, haka za ta ci gaba da ruruwa wasu ma har ta kai ga ta zama rikicin dangi.
Wanda a tawa fahimtar abu na farko da ke kawo afkuwar hakan shi ne kishi, wanda ke damun wasu matan har ta kai da an haifar da rarrabuwar kawunan yara.
Musamman idan muka yi duba ta bangaren cikin gida, ta yadda idan ya zamo matar gidan ta haura daya, hakan na afkuwa ta dalilin nuna soyayya ko fifiko ga maigida da yake nuna wa yaran daya daga cikin, wanda hakan ke sa iyayen sauran yaran su fara nuna kishi da kuma kokarin ziga yaran nasu.
Wani maigidan kuma na iya bakin kokarinsa wajen ganin ya yi wa yaran komai daya bisa adalci kishi na mata ke sa daya daga ciki nuna rashin kyautatawa na ta tafi so iya nata kawai za a kyautatawa har ta kai da ta fara yi wa yaran wani nuni na daban da zai zauna a zuciyarsu har girmansu.
Ta wani bangaren kuma mace daya ce a gidan, amma kuma yaran sam! basa jituwa wanda yake zamowa har magana ma ba sa yi wa juna, ta hanyar hada su da ka yi ko mutanen unguwa, ko wasu daga cikin ‘yan’uwa ko matansu, ko makamancin haka.
Wasu kuma hakan na faruwa ne ta dalilin gurbatacciyar zuciya da daya daga cikin yaran yake da shi na hassada ko kyashi ko makamancin haka.
Hakan na faruwa ta hanyoyi daban-daban wanda wajen yayi kadan a zayyana. Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan matsala, ko me yake kawo rarrabuwar kai tsakanin ‘yan’uwa na jini?, Ko laifin waye tsakanin iyaye da yaran da wasu mutanen daban?, wanne matsaloli hakan ke haifarwa?, ta wacce hanya za a magance afkuwar hakan?.
Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Abdul’azeez Yareema Shaheed (Dan Amar) daga Jihar Kano:
an’uwa na jini shi ne; son zuciya da kuma fifita daya daga cikin ‘Ya’yan da wasu iyaye ke yi, su fi son wani ko wata daga cikin yaransu hakan na haifar da rarrabuwar kai a tsakanin ‘yan’uwa na jini. Gaskiya laifin iyaye ne, wasu sai su fifita son wasu daga cikin yaransu.
Hakan na kawo matsalar gaba, kyashi, yanke zumunci da juna. Hanyar da za a magance afkuwar hakan shi ne; Iyaye su tsaya tsayin daka su so ‘ya’yansu tsakani da Allah kar su nuna sun fi son wani ko wata a tsakaninsu. Ina ba da shawarar da mu yi hakuri mu so junanmu domin Allah, kuma mu dinga hakuri da ‘yan’uwanmu ako da yaushe.
Khadija Muhammad Sha’aban daga Jihar Kano:
iyayensu na fifita daya daga cikin yaran ne, kirikiri za su dinga nunawa a gaban kowa sun fi son wannan akan sauran yaransu, ta haka ne sai ki ga tsana ta shiga tsakaninsu da ‘yan’uwansu, har ta kai ga suna gaba da juna, ba sa kaunar junansu ko kadan.
Laifin na iyayen ne, dan da suna nunawa yaran nasu dukkansu gaba daya suna kaunarsu, hakan ba za su dinga faruwa ba, jan yaro a jiki yana sa ya dinga fada miki duk wasu sirrinsa da yake boyewa.
Abin da hakan ke haifarwa kamar yadda na fada a farko shi ne; zai sa ka dinga tsanar dan uwanka ka ji ba ka son ci gabansa kwata-kwata, duk wani wanda zai kawo masa ci gaba ka dinga kokarin ganin ka toshe shi. Iyaye su dinga nunawa yaran dukkansu daya suke, hakan shi ne zai magance wannan matsalar, ko da akwai wanda suke so cikin ransu, su rike shi a ransu ka da su sake su bayyana ko su nuna, kuma hakan na iya janyowa yaransu shiga tunani Anya su suka haifesu kuwa?.
Shawarata anan ita ce yara dai gaba dayansu kai ka haifesu, bai kamata a dinga nuna bambanci a tsakaninsu ba, hakan na iya jawo matsaloli babba a duk lokacin da suka ankara da cewar iyayensu sun ware wani daban wanda suka fi so, bayan su ma yaransu ne, da fatan masu irin wannan halayyar za su gyara.
Fadeelah Yakubu (Milhaat) daga Jihar Gombe:
Idan ka ga yara sun hada kai suna son junansu ko kuma akasin hakan, ba gargada laifin iyaye ne, iyayen mu suna wani kuskuren da suna daukar hakan a matsayin soyayya kuma ba haka bane ba, mun sani dole ne akwai dan da zai fi soyuwa a ranka amma kuma yana da kyau ka boye, idan yaro ya ga ka fi son dan uwansa akansa dole ne ya tsane shi.
Laifin iyaye ne, sabida sun fi kusa da ‘ya’yansu fiye da kowa, so su ya kamata su jasu a Jiki su nuna musu soyayya sannan su basu kulawar da ta dace.
Kamar yadda nace a farko hakan yana sanya su ji sun tsani dan uwansu, wani kam ma har ya kai ga kisa, ko kuma ya cutar da shi ta hanyar da ba a za a taba tsammani ba.
Iyaye maza da Mata gare ku, kar ku yi kuskuren fifiko a tsakanin yaran ku, Ku kaunace su, sannan ku jasu a jiki, ku nuna musu muhimmancin hadin kansu.
Aliyu Idris Author, Jihar Jigawa (Sarkin Yakin Malumman Matazu) 07032229525:
Rarrabuwar kai ko kuma juna a tsakanin yaran da suke uwa daya uba daya a halin yanzu ya zama tamkar ruwan dare ne a ko ina a fadin Najeriya, kuma kowa ya san wannan ba kuma bakon abu ba ne a tsakanin ‘yan’uwan juna a rayuwar yanzu da muke ciki.
Yin hakan yana faruwa ne ta fuskoki da dama a sakamakon rashin kula da kuma karancin jajjirecewar iyaye, musamman ma a wajen ginawa yaransu tarbiyya mai kyau.
Iyaye a har kullum suna iya canja dabi’un ‘ya’yansu ta hanyar nuna musu bambanci ko kuma wariya a tare da su, iyaye suna iya ba da kyauta daga wasu a cikin ‘ya’yansu har ma sai ka ga sun bar wasu ba tare da sun basu ba, bambancin so ko nuna kauna a tsakanin yara, nuna tsana ga iyaye daga cikin wasu a ‘ya’yansu da sauran nuna fifiko da dama a tsakanin ‘ya’yansu ta bangare daban-daban.
Idan har iyaye za su ci gaba da aiwatar da irin wannan hali a tsakanin ‘ya’ya, to dole matsalar rashin kaunar juna ta samun wajen zama a tsakaninsu da ci gaba da yaduwa a tare da su ba tare da samun masalaha ba.
Shi wannan laifin duka zai iya shafar rayuwar kowa a tsakanin al’umma, idan har babu kyautatawa a tsakanin juna da nuna kyama daga wasu iyaye, to yin hakan zai iya haifar da wani abu marar kyau a zahirin gaskiya.
Saboda su iyaye wannan laifi ko al’amari zai fi shafarsu a har kullum, duba da yadda suke nuna bambanci a tsakanin ‘ya’yansu yin hakan laifin yasa za a iya dora laifin ga iyaye gabaki daya feye da kowa ma.
Yin hakan yana iya haifar da kalubale da dama a cikin yara da al’umma, musamman kara samar da rashin daidaito da sake yaduwar gaba a tsakanin ‘ya’yansu, sannan da sake shigar da su hanyar kangarewa da fadawa harkar banza wacce za ta iya haifar da damuwa a tsakanin al’umma da dama, sannan kuma daga karshe ‘yara su iya samun kansu da mummunar dabi’a ta hanyar da ba a yi zato ba.
Dole ne iyaye su ci gaba da kula da yaransu ta fuskoki da dama, da nuna musu zumunci da kuma son ‘yan’uwan juna a tsakanisu.
Sannan kuma iyaye dole ne su kara kaimi, musamman ma a wajen kara gina tarbiyyar ‘ya’yansu a ko da yaushe.
Iyaye dole su gujewa nuna fifiko a tsakanin ‘ya’yansu a har kullum, kuma yana da kyau dole iyaye su ci gaba da jan hankalin ‘ya’yansu da yi musu nasiha mai kyau, da kuma yin kokarin zaunar da su wajen yi musu sasanto a duk lokacin da suka ga matsala a tare da ‘ya’yansu a ko da yaushe.
Ni shawarata da zan ba da a nan shi ne; iyaye su yi kokarin sauke nauyin da Allah ya dora musu a tsakani a kan ‘ya’yansu da suka haifa.
Ta hanyar basu tarbiyya mai kyau da kuma saka su a kan hanyar neman ilimi a ko da yaushe, sannan yin hakan zai taimaka musu su daina gaba da kin juna a tsakaninsu a har kullum.
Domin shi ilimi yana iya kore jahilci a har kullum da kuma rage gaba da nuna kin juna a tsakanin ‘ya’ya da al’umma gabaki daya.