Wannan ita ce karshen tattaunawa da Jarumi SANI ABUBAKAR da muka fara kawowa a makon da ya gabata tare da wakiliyarmu, RABI’AT SIDI BALA. A karanta har karshe don jin abubuwan ta kunsa kamar haka:
Tun daga farkon farawarka kawo yanzu wanne irin kalubale ka fuskanta cikin masana’antar?
Shi kalubale ba a rasa shi, a gaskiyar magana tun daga farko kawo yanzu ba zan iya cewa ga wani babban kalubale dana hadu da shi ba face rashin kasuwa, yadda sana’ar ta canja ba yadda take da farko ba akalarta ta juya ta yi canji kala-kala, wannan canji da ta kawo bangaren kasuwa shi ne kawai kalubalen. Sannan babban abin da ya fi damu na shi ne za ka ga mutum ya fito ya ci zarafinmu amma ba mu da ikon ramawa su ma shuwagabanninmu sai dai kawai su zuba ido saboda gudun kar mutum ya zo yayi magana wani ya fadi maganar da hankalinka ba zai iya dauka ba, gaskiya wadannan shi ne matsalolin da nake ganin su ka fi damuna. za ka ga mutumin da bai ma san ya sana’ar taka take ba, bai ma taba zuwa ya ga ya ma ake sana’ar ba, bai san ya aka fara ta ya ake kare ta ba, amma za ka ga ya fito yana cin mutunci, ko cin zarafi yana zaginku a cikin masana’antar, kuma karshe dai abu daya kawai za a yi a ce a yi hakuri. Babu wata masana’anta ko wajen sana’a da za ka tarar ana zagin mutum ko ana cin zarafinsa kuma babu yadda zai yi sai masana’antar Kannywood. Ni dai tunda nake cikin masana’antar babu wani wanda ya taba daukar wani tallafi ya ce ga wani tallafi an ba da domin ci gaban masana’antar in dai ba maigidana ba, na tabbatar sanata ya taimaki ‘yan kannywood wanda kuma duk abin da aka yi kusan da hannuna ma a ciki, amma kalubale na cin mutunci da cin zarafi dai muna gani.
Ba ka ganin wasun cikinku ne ke nemo muku zagin, ta yadda suke tafiyar da nasu al’amuran har ta kai da an yi muku kudin goro, ko ya abun yake?
Gaskiyar magana guda daya ita ce; duk cikin al’ummar da ki ka gani, kuma kowacce irin masana’anta a duniya dole akwai bata gari a cikinta kuma akwai na kirki, dan haka babu yadda za a ce mu wankakku ne dan muna wannan maganar, a’a! dole akwai bata gari a cikinmu. Amma maganar na ce wani ne yake janyo mana zagi a’a! ai bai kamata ka yi shari’a ba tare da, ka san me ye yake faruwa ba. Dole a cikin al’umma idan kana sana’a sai ka tarar da bata gari da zai ja maka zagi wannan kuwa mun sani, hatta a cikinku ‘yan jarida ku kun sani akwai wadanda bata gari ne suke ja muku zagi akan sana’arku, ba za ku ce ku a cikin sana’arku babu mai zaginku ba, a kowacce sana’a ana zagin mutane.
Na ji ka ce ba wanda ya taba ba ka wani tallafi a masana’antar, to ya batun kallon da sauran jama’a ke yi wa ‘yan kannywood na cewar; suna tafiya ne da gwamnati, yayin da jam’iyya tayi nasara tana ware musu wasu kudade na daban, me za ka ce akan hakan?
Gaskiyar magana shi dan fim zai iya yin siyasa, misali; kamar ni kin ga tunda nake da maigidana nake tafiya tare da shi, ni ba jam’iyya nake bi ba, bayan zaben maigidana zan duba na ga wa ya cancanta na zabe shi?, kuma ni bana bin wani dan siyasa bayan maigidana, akwai masu yin hakan amma akwai wanda ba sa canja jam’iyya a ‘yan kannywood din. Kuma dole ai dan fim yayi siyasa saboda siyasa ta kowa ce dole ka duba ka ga ya za a yi al’ummarka ta zama gyararriyar al’umma?, misali; dole ka duba ka hanga ka gani wane ne zai taimaki al’umma, inda gudunmawar da za ka ba shi kai ma ka bada taka irin gudunmawar, ni kin ga Barau Jibril Maliya ne maigidana, dan haka dole ina bin sa dan na tabbatar da cewa inada yakini dari bisa dari yana kyautatawa al’umma.
Ya batun nasarori fa, wanne irin nasarori ka samu game da fim?
Sai dai na ce Alhamdulillahi dan ban isa ma na ce ga iyakacinsu ba, an same su da yawa burjik kuma ana kan samu, dan cikin sana’ar Allah ya rufa ma asiri ai ka gama samun nasara, an samu nasarori babu iyaka gaskiya.