Kwararren likitan kashi da kwakwalwa a asbitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da asibitin Dala (NOHD), Dakta Musabahu Haruna ya bayyana cewa a wani lokaci suna kallon majinyaci zai mutu amma su kasa taimakonsa sakamakon rashin kayan aiki na zamani.
Dakta Musabahu ya kasance sabon mataimakin shugaban kungiyar likitocin kashi ta Nijeriya daga Arewa (NSS), ya bayyana cewa karancin sayan kayan aiki daga gwamnatin Nijeriya da rashin kulawa da sauran matsaloli da suka adabi wannan fannin ya sa a wani lokaci, suna kallon majinyaji idan aka samu wani dan lokaci kadan ba a yi masa aiki ba a iliman ce zai iya mutuwa, amma ba yadda za suka yi taimake masa saboda rashin kayan aiki na zamani.
- An Kwantar Da Tsohon Shugaban Sudan Omar al-Bashir A Asibiti
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Rage Kudin Sufuri Da Kashi 40 Ta Hanyar Amfani Da Motoci Masu Iskar Gas
A cewarsa, abun takaici shi ne idan an dauko wani dan gata ko jami’in gwamnati an kai shi kasar Turai, kudin da ake kashe wa majinyacin ya isa a yi wa sama da mutum 100 aiki, amma an kai kudin waje.
Ya kara da cewa dole ne ya sa likitocin Nijeriya suke ficewa daga kasar zuwa kasashen Turai, domin samun wurin aiki mai kyau da albashi mai tsoka ba tare da wata matsala ba.
Dakta Musubahu ya ce su dai a bangarin kungiyarsu ta NSS sun yi wa mutum 16 aikin taimako, inda marasa lafiya suka biya rabin kudin aikin, sannan kungiyar NSS ta biya rabi, saboda tsadar kayan aiki.