Tarbiyya wata abu ce wadda ake fara koya ma ‘ya’ya tun suna kanana da za su fara samu daga gida wurin Iyaye wadanda sune suke zama Malamai na farko da suke fara koya ita tarbiyyar.
Idan suka fara da farar saka wato tarbiyyar data dace su rika koyawa su biyu,wannan kuma ba sai an bari ‘ya’ya sun fara girma ba sannan ace ana son dole ne sai sun fara tafiyar da ake son su yi.
- Yadda ‘Yan Bindiga Suka Hallaka Ma’aikata Hudu Da ‘Yansanda Biyu A Kamfanin Sarrafa Tasa
- Ko Makiyan Buhari Sun San Aikin Da Ya Yi Yafi Na Gwamnatocin Baya -Minista
Idan aka yi haka ko hakan ake yi wannan yana nuna ke nan an baro shiri tun rani ke nan, domin kuwa shi Icce tun yana dan karami ne ake tankwara shi cikin sauki amma idan har aka bari sai da ya girma sannan ace za ayi,to ko an so a tankwara shi karyewa zai yi ko a karya shi.
Hausawa sun ce tarbiyya daga gida ake fara ta, idan kuma abin ya kasance ba a fara yin ta daga gida ba, to fa an zo wurin da shiga matsala ke nan.
Idan gida suka fara dora tubalin tarbiyya maikyau ga ‘ya’yansu,wannan ya nuna sauran Malaman tarbiyyar ba za su sha wata wahala ba. sauran Malaman tarbiyya da suka hada da Unguwa da Makarantu ba za su hadu da wata matsala ba.
Amma abinda ke faruwa yanzu shi ne wuraren koyar da tarbiyyar da suka hada da Gida,Unguwa,da Makaranta, aiki ya yi ma kurege yawa ne saboda babbar makarantar Malaman da suka dace su fara dora tubalin rayuwa sun kasa yin abinda ya dace ace sun fara yi.
Shi yasa wasu daga cikin yaran ko ‘ya’yan da suka tashi cikin irin wannan turbar rayuwar su ne ke zabar ma kansu irin rayuwar data dace su yi, saboda basu da wasu jagorori an barsu ne hakanan sakaka su ke zabar ma kansu abinda ya dace su yi a rayuwar tasu.