Wasu ‘yan bindiga da ba a san kosu wane ne ba sun kai mummunar hari a kamfanin sarrafa tasa da ke Ajaokuta a Jihar Kogi, inda suka hallaka mutum shida da suka hada da ma’aikata ‘yan kasashen waje biyu da direbobin kamfanin biyu da kuma jami’an ‘yansanda biyu tare da garkuwa da ma’aikata uku ‘yan kasashen waje da ke aiki a kamfanin.
Harin ya zo ne bayan makonni biyu da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Jida Bassa da ke yankin karamar hukumar ta Ajaokuta, inda suka hallaka ‘yan sanda uku da ‘yan sintiri (bijilante) biyar da kuma sace yara uku a rukunin gidaje na Kaduna da ke kamfanin sarrafa karafa na Ajaokuta, inda suka nemi a biya su kudin fansa har naira miliyan dari kafin su saki kananan yaran uku wadda shekarunsu suka kama daga biyar, bakwai zuwa goma.
- Ziyarar Babbar jami’ar Lithuania A Taiwan Shirme Ne
- Dariye Zai Tsaya Takarar Sanata A Filato Bayan Yi Masa Afuwa Daga Gidan Yari
Wata majiya ta shaida wa Jaridar LEADERSHIP Hausa cewa ‘yan bindigan sun shigo kamfanin sarrafa tasan da ke karamar hukumar Ajaokuta na Jihar Kogi ne da misalin karfe bakwai na daren ranar Juma’ar da ta gabata, inda suka kashe ma’aikatan kamfanin hudu da ke cikin motar bas da ke shirin kai su wurare dabam-dabam.
Wani ganau wanda ya nemi a sakaye sunansa ya ce ‘yan bindigan wadanda suka kawo harin cikin motoci biyu, sun yi wa ma’aikata ‘yan kasashen wajen da sauran ma’aikatan dak e cikin motar kamfanin kwantar bauna, inda suka fara harbin kan mai-uwada-wabi.
Ya ce, “Yau wata ranan bakin ciki ne garemu a nan Ajaokuta, muna cikin jimamin kashe jami’an tsaro bakwai da ‘yan bindiga suka yi a Jida Bassa kwanan nan da yin garkuwa da yara uku duk a nan Ajaokuta, sai gashi kuma wannan ya auku, to yaya za mu yi da rayukannu?
“Wadanda suka rasa rayukansu da wadanda ‘yan bindigan suka yi garkuwa da su suna shirin barin kamfanin ne zuwa masaukinsu da ke rukunun gidaje na Neja da ke Ajaokutan kafin ‘yan bindigan su yi musu kwantar bauna.
Ya ce, “Suna aiki ne a kamfanin sarrafa tasa na yammacin Afirka da ke nan Ajaokuta.
“Jami’an ‘yan sanda sun rika musayar wuta da bata-garin, amma abin takaici biyu daga cikin ‘yan sandan da direbobin kamfanin guda biyu da kuma ma’aikata ‘yan kasashen waje, sun rasa rayukansu a cikin motar kamfanin, a yayin da kuma ‘yan bindigan suka yi garkuwa da ma’aikata ‘yan kasashen waje uku,” in ji shi.
A bangare guda kuma, kwamishinan watsa labarai na Jihar Kogi, Mista Kingsley Fanwo, a martanin da yayi game da harin ya ce gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da wannan harin.
Ya kuma kara da cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ceto wadanda aka yi garkuwa da su da kuma zakulo wadanda suka aikata wannan mummunar aiki.
Kwamishinan ya kuma ce wannan hari da sauran ayyukan bata-gari ko kadan ba zai karya wa gwambatin Jihar Kogi karkashin shugabancin Gwamna Yahaya Bello wajen kare lafiya da kuma dujiyoyin al’umma, sannan ya gargadi masu aikata laifufuka da su gaggauta sauya wani wurin don aikata laifi.
Haka shi ma kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kogi, CP Edward Egbuka, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kogi, Mista William Aya a wata sanarwa da ya fitar, ya ce rundunar ta fara bincike game da faruwar lamarin kuma a shirye take ta zakulo wadanda suka aikata danyen aikin.
Kawo hada wannan labarin, ‘yan bindigan ba su tuntubi iyalai ko kamfanin sarrafa tasan ba domin amsar kudin fansa.