Aishatu Buhari, uwargidan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana yadda ta yi rayuwa na shekara 8 a fadar shugaban kasa a tattaunawar da ta yi BBC, ga dai yadda hirar ta kasance kamar yadda wakiliyarmu Bilkisu Tijjani Kasim ta nakalto mana.
Za mu so mu ji cewa a cikin shekaru takwas da kuka kwashe a kan mulki kun cika alkawuran da kuka dauko wa ‘yan Nijeriya?
Alhamdulillah mun gode wa Allah da ya nuna mana karshen shekara takwas mun gama lafiya ai mun gode wa Allah, to maganar cika alkawari to mun dai yi iyakacin kokarimmu gorgwadon abin da zamu iya yi kuma idan za a hada mu da gwannatin da muka zo muka tadda wanda muka karba hannun su kila mun yi kamar kashi casain da biyar in kuma za a duba da kuzarin da muka zo na yin aiki wa ‘yan Nijeriya wata kila mun samu kashi hamsin.
A cikin shekaru takwas da kika kwashe a wannan fada ta shugaban kasa a bila wane abu ne zaki iya tunawa da ya tsaya miki a ranki walau na farin ciki ko na bakin ciki da ya tsaya miki a ranki a wannan gida?
Eh to sai dai mu ce alhamdullih, farin ciki dai sai dai kwanan nan da muka yi da yara da aka auna su aka ce duk za su mutu saboda akwai wani huji da aka ce ana haihuwar yara dashi
Yayan ki ke nan kike magana?
Aa ‘ya’yan mutane “yan Nijeriya. Muka dibi yara guda goma muka shigo da wasu turawa muka shigo dasu daga Itali su goma sha daya suka zo suka yi aiki to dama mun fi ganin yaran da suke da huji din a zuciyar su guda daya to dama yaran da suke da hujin a zuciyar su ko wanne yana da guda hudu a zuciyarsa aka zo aka rufe musu gaba daya kuma sun rayu sun tashi sun koma makaranta to gaskiya idan na tuna wannan yana faranta min rai so sai.
Wane abu ne da zaki tuna wanda yake bakanta miki rai?
Lokacin da maigida na bashi da lafiya.
Wane hali kika shiga kina jin tsoran cewar abun da yasamu marigayi ‘Yaraduwa zai samu Shugaba Buhari shi ne abin da ya firgita ki?
A,a ba haka ba ne mutuwa bata da magani amma wahala ne ake gudu saboda na riga na basu shawarwari don ni kade nake kula dashi kafin mu zo nan kuma ya zo nan lafiya kalau na zo na basu shawarwari da za su bi saboda ya ci gaba da samu lafiyar shi, shi bai ji maganar ba kuma suma basu ji ba shi ne ya daga min hankali.
A tunaninki mai ya sa basu ji maganar ki ba ko kuma shawarar da kika basu?
To suna ganin mata basu isa su gaya musu ba tunda suna ganin suna kan milki da kuma wadanda suke tare dasu suna ganin mata basu isa su gaya musu su ji ba saboda suna ganin abinda muke fada duk tatsuniya ce sai da ya kwanta ciwo ruf duk gaba daya suna kallon shi shi yasa ko a lokacin na yi magana astaghafililla na san ba mutuwa zai yi ba sai dai ya sha wahala kuma gashi ya tashi.
A cikin wadannan tsawon shekaru takwas akwai wani abu da zaki iya tunawa wanda ki ke jin da kin sani akansa wanda baki yi shi ba?
Babu duk abinda zan yi Allah ya riga ya tsara haka zan yi.
A hirarki da BBC farkon fara shugaban cin Nijeriya hirar nan ta tada kora so sai saboda ta janyo cece kuce da dama saboda ana ganin abubuwan da ki ka fada kamar bai kamata ki fade su ba kina danasani yin wannan hirar?
A,a ko daya.
Wani bai zo yace miki mai yasa kika yi ba ko kuma shi maigida bai miki magana ba?
To mutane dai suna maganganun sune dai a waje shi dama ya san zan iya fadin maganganun duka.
Saboda haka baku samu matsala da shi ba a kan wannan hirar?
Ko daya bamu samu matsala dashi ba a kan wannan hirar ko daya bamu samu ba.
Shi abunda ma ya bashi haushi da mutane suke cewa don na yi tafiya na tafi Landan, naje na duba yara sai mutane suke cewa ya sakeni na tafi ya sakeni na tafi to sai ya yi fushi wai naji mutane suna fadi haka ban dawo ba sai nace don mutane suna fadi haka shi ne zan dawo ina ruwana dasu naci gaba da zamana.
Bari mu tabo wani batu da mutane suke sunji wace iri alakace da take tsakanin ki da sabon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da iyalansa?
Eh shi maigidana dama yana dama suna magana a kan siyasa amma ni bantaba zama kusa dashi ba sai 2015.
Lokacin da kuka zo mulki kenan?
Eh 2014 ne da aka bashi tikiti na zaban shugaban kasa shi ne a lokaci aka gani kamar kin san za a bawa mai dubasu kwararru ko? su auna su, su gani zai iya cin zabe ko ba zai iya ba to a lokacin ne sai aka auna aka ce an gaji da ganinsa shi kade yana kamfen sai an gama ya je kotu sau uku aka yi wannan aka gama a kudancin Nijeriya sun dauka shi mutunne wanda yake da a kida ta rike da abin addinin musulunci da sauransu amma a arewacin Nijeriya zai iya cin zabe amma kudancin Nijeriya ba zai iya kawowa ba to ya za a yi da shi, shi ne an zauna an auna duka mutanan da suke tare dashi da wanda ya ke da girma ko karfin da zai iya kawo musu kuri’u wanda zai cika kundun tsarin mulkin kasa yadda ya fadi asamu kashi ishirin da biyar kowanne jiha kai kuma ka kawo bangaran ka ko wasu jihohi ka kawo kashi ashirin da biyar lokacin ne Tinubu ya kirani ya ce a Hajiya dole sai kinsa mana hannu inba haka ba ba zamu kai labari ba ya ce sau hudu muna bawa mutane suna dubawa duka sun gaya mana abu daya suka ce dole ne sai mun hada da iyalansa da aka bincika tarihin iyalansa ya suke ‘yan yansa mata ne suna karatu bawan da yake da matsala da sauransu kuma matarshi ta je makaranta ta yi digiri ta yi mastas tasan abun da take yi tana gudanar da harkokin kasuwancin ta dai dai gwurgwado don haka idan tafita ta yi magama mutanan kudancin Nijeriya dole za su saurara sai aka zo aka gayawa maigidana aka ce masa ga abin da ake so ayi sai yace kai shi baya so matarshi ta fita ya gaya min nima nace bana so na fita to daga baya kamar su aminci da sauransu su kace Janarar bawai muna maganar kai ne shugaban kasa ba ko da kayi shugaban kasa ba a a dole ne ka hau saboda mu mun riga mun kawo kanmu wurinka, saboda idan wani jam’iya ce ta ci to rayuwarmu za ta shiga cikin hatsari to shi ne ya jajirce a kan dole ne na fita sai ya ce to idan na fita na je kunkiyoyi biyu ko uku sai nace to ni zan tura mata su wakiltani.
To idan dai na fahince ki alakarki da Bola Ahmad Tinubu ta fara ne tun daga shekara ta 2014 wato a lokcin kamfen?
Eh haka ne.
Yanzu da ya kasnce ke zaki fita ita Misis Remi za ta shigo ranar da kika zagaya da ita cikin fadar shugaban kasa taga wuraran da ke kike muamala ya kike ji a ranki?
To nidai ina Alhamdulillahi nidai zan fita daga nan wurin da raina maigidana ma da ranshi wanda ya yi hatsari kusan ya mutu ya dawo da ranshi to mun gode wa Allah na ji dadi, Allah ya nuna mun ranar da zan fita lafiya lau, da farin ciki nima har ina nunawa wata ga yadda wajen yake.
Yanzu idan misali idan kika fita daga cikin fadar nan za a dinga yawan ganinki tare da ita matar sabon shugaban kasa idan ta bukaci shawarar ki ko taimako?
To kila idan ta bukaci shawarana na bata amma baza a dinga gani na da ita ba don lokacin dana yi ni kade na yi itama haka ta yi nata ita kade aikin fes ledi
Lokacin da aka tsaida Bola Ahmad Tinubu a matsayin dan takara a jam’iyar APC an yi ta surutai kan cewar a kan akwai wadansu mutane dake nan bila da basa so kinsan wannan bayanin?
Eh nasani har yanzu ma basa so
Wace rawa kika taka a wannan lokacin?
Suka ce wai jam’iyya duka tayar da an fitar da mutum wanda baya cikin tsarin fatin wannan zai jawo tashi hankali da raba kan mutane fatin za ta rugurguje shi ne na cewa shi ne na cewa Garba Shehu mai maigidana ya fadi kan wannan maganar ya ce shi ba ruwan shi, shi bai ce a zabi mutum ba aje ayi zaben fidda gwani.