Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu kan gazawa wajen magance matsalar tsaro. Ya bukaci ya jefar da kwallon mangwaro domin ya huta da kuda.
Atiku ya kasance dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya dai bayyana takaicinsa ta yadda ake samun karuwar garkuwa da mutane da kuma kasha-kashe a ko’ina a fadin kasar nan.
- Mafarauta Sun Karɓi Ƙorafe-ƙorafe 19 Cikin Watan Janairu A Kano
- Gwamnatin Filato Ta Kafa Kwamitin Mutane 10 Don Shawo Kan Matsalar Tsaro
Ya dai yi takaicin yadda aka kashe wata matashiya tare da mahaifiyarta a Abuja da kuma kisan sarakuna biyu a Jihar Ekiti a ranar Litinin.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya yi mamakin yadda shugaban kasa ya jilla zuwa kasar Faransa ba tare da daukar mataki kan ‘yan bindiga da kuma sauran ayyukan ta’addanci da ke faruwa a kasar nan.
A dai ranar Laraba da ta gabata ce, Shugaban kasa Tinubu ya zai ziyara ta musamman a kasar Faransa.
A shafinsa na sada zumunta, Atiku ya rubuta cewa, “Tinubu bai damu da halin da Nijeriya ke ciki ba na rashin tsaro. Abun mamaki fa shi ne babban kwamandar askarawan kasar nan, amma har zai iya yin wata ziyara ta musaman a wannan yanayi da ake fama da rashin tsaro a Nijeriya.
“A daidai wannan lokaci, masu garkuwa da mutane sun kashe wata matashiyar likita tare da kakarta a Abuja sakamakon gaza biyan kudin fansa na naira miliyan 90. Sannan sun kashe sarakuna guda biyu a Jihar Ekiti, dadai sauran ‘yan Nijeriyan da aka kashe da bazan iya lissafawa ba.
“Idan har matsalar ta gagare ka ne, to ka kama gife akwai masu iyawa. A halin yanzu ‘yan Nijeriya ba sa bukatar shugaba mai son shakatawa.
“Kasar nan na bukatar shugaban da zai iya aiki na tsawon awanni 24 na kowacce rana, domin magance rashin tsaro da kuma durkushewar tattalin arziki.”