Kungiyar Masu Sana’ar Baburan Acaba ta Kasa (ACOMORAN), ta yi gargadin cewa shirin hamrata sana’ar acaba zai sa ‘yan Najeriya miliyan 40 su rasa aikin yi.
Kungiyar ta ce hakan na iya haifar da karin ayyukan ta’addanci a fadin kasar nan.
Idan dai za a iya tunawa, Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana cewa majalisar tsaro ta kasa karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta yi bayanin cewa za a iya tilastawa gwamnati ta hana amfani da baburan acaba kamar yadda ta saba.
An gano cewa amfani da baburan na daga cikin hanyoyin da ‘yan bindiga ke yi wajen aikata garkuwa da mutane.
Malami ya kara da cewa wadanda ke amfani da babura a matsayin sana’a ba su kai kashi 20 cikin 100 na al’ummar kasar nan ba, ya kara da cewa za a iya sadaukar da su, “Ina ganin sadaukarwar ba ta yi yawa ba kuma ya cancanci a yi la’akari da hakan.
Da yake jawabi ga taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, shugaban kungiyar ACOMORAN na kasa, Samsudeen Apelogun, ya bayyana cewa mambobin kungiyar sun kai miliyan 12 a fadin kasar nan, inda miliyan shida ke da rajista.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi watsi da manufar hana amfani da babura a fadin kasar nan, domin hakan ba zai haifar da da mai ido ba.
Hakazalika, Apelogun ya yi gargadin illolin tattalin arziki da tsaro, inda ya ce baya ga talauta miliyoyin ‘yan Nijeriya, hakan zai kara dagula munanan dabi’u da gwamnatin da ke kokarin shawo kansu game da matsalar tsaro.