Majalisar dattawa a ranar Talata ta yi kira ga rundunar sojin Nijeriya da ta gaggauta tura jami’anta da sabbin kayan yaki na zamani zuwa jihohin Borno da Yobe sakamakon sabon hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai a yankin.
An yi wannan kiran ne biyo bayan sabbin hare-haren ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, ciki har da kashe sojoji sama da 10 a garin Marte da ke karamar hukumar Monguno ta jihar Borno, a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu.
- Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya
- An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya
‘Yan ta’addan sun kuma sake kai wani hari da sanyin safiyar Talata a Gajiram – hedkwatar karamar hukumar Nganzai.
Kudirin wanda Shugaban mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Tahir Munguno ya kawo kudirin, ya yi takaicin yadda ayyukan ta’addanci ya sake dawowa, wanda a baya aka samu zaman lafiya sosai a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp