A ranar Laraba ne daruruwan matasa suka tare hanyar Auchi-Igarra-Ibillo ta jihar Edo, domin nuna rashin amincewarsu da lalacewar hanyar da suka ce ta janyo yawaitar sace-sacen jama’a da rashin ababen more rayuwa.
Masu zanga-zangar sun yi korafin cewa, garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a kullum saboda munanan hanyoyi da kuma rashin isassun ababen more rayuwa.
Sun kuma yi tir da cewa, masu rike da mukaman siyasa daga yankin ba su damu da halin da jama’a ke ciki ba.
Zanga-zangar ta haifar da cunkoso a kan hanyar yayin da matafiya da suka hada da manyan motoci a kan titin suka tsaya cak na tsawon sa’o’i.
Matasan sun kuma koka da yadda har yanzu ba a sako wani jigo a jam’iyyar LP ba, Okasime Olowojoba da aka yi garkuwa da shi kusan wata guda duk da biyan sama da Naira miliyan 5 kudin fansa.
Daya daga cikin masu zanga-zangar Paul Lawani ya ce, “Ba za mu iya ci gaba da zama bayi a kasarmu ba, ya kamata gwamnati ta fada mana abin da take yi.”