Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya yabawa rundunar sojojin Nijeriya, DSS, ‘yansandan Nijeriya da sauran jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi na dakile barazanar tsaro.
Ribadu ya kuma ce sanya ido tare da hadin kan ‘yan Nijeriya ya taimaka wajen yaki da ta’addanci, da sauran matsalolin tsaro.
- ‘Yan Bindiga Ne Suka Kawo Cikas Ga Samar Da Isasshiyar Wutar Lantarki Ga ‘Yan Nijeriya A 2024 – Minista
- PDP Ta Nemi Tinubu Ya Binciki N25trn Da Ake Zargin Shugabannin APC Sun Sace
Ribadu ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Laraba, a cikin sakonsa na sabuwar shekara da ya gabatar ta hannun kodinetan hukumar yaki da ta’addanci ta kasa (NCTC), Manjo janar, Adamu Laka.
Ya yi nuni da cewa, nasarorin da aka samu a kokarin inganta tsaron kasa, sun samo asali ne daga hadin kan ‘yan Nijeriya, sadaukar da kai na jami’an soji, da sauran jami’an tsaro da kuma na jami’an leken asiri.