Ɗan wasan gaban Manchester United, Rasmus Højlund, ya kammala komawa ƙungiyar Napoli a matsayin aro, tare da zaɓin siya nan gaba idan sun gamsu da bajintarsa.
Jimillar yarjejeniyar ta kai Yuro miliyan 45, ciki har da Yuro miliyan shida na kuɗin aro, sannan Napoli za ta biya sauran idan ta samu gurbin shiga gasar zakarun Turai.
- Hukumar SUBEB Ta Yi Kira Ga Al’umma Da Su Sa ‘Ya’yansu Makaranta
- Cire Tallafin Wutar Lantarki Zai Kara Kuntata Rayuwar ‘Yan Nijeriya – Kungiyar Kwadago
Fitaccen masani kan harkokin ƙwallon ƙafa, Fabrizio Romano, ya tabbatar da wannan a shafinsa na X, inda ya ce an riga an ƙulla yarjejeniyar.
Højlund ya nuna sha’awar barin United saboda ƙarancin damar samun buga wasa a ƙarƙashin sabon koci, Ruben Amorim, bayan zuwan sababbin ‘yan wasa kamar Matheus Cunha, Benjamin Sesko da Bryan Mbeumo.
A cikin sa’o’i 24 masu zuwa ake sa ran za a yi masa gwajin lafiya.
Ɗan wasan ɗan shekaru 22 ya zura ƙwallaye 10 ne kawai a wasanni 52 da ya buga a United bara, kuma zuwan Sesko ya ka5ra rage masa damar zama a cikin ƙungiyar.
Sha’awar Napoli kan Højlund ta ƙaru ne bayan Romelu Lukaku ya samu rauni a cinyarsa wanda zai sa ya daɗe a jinya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp