Kungiyar Gwamnonin Arewacin Nijeriya ta bayyana alhininta kan rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari, inda ta bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi a ƙasa baki ɗaya.
A cikin saƙon ta’aziyya da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, gwamnonin sun yabawa shugaban wajen jajircewa da gaskiya da kuma hidimtawa ƙasa.
- Tinubu Ya Tabbatar da Rasuwar Buhari, Ya Tura Shettima Zuwa Landan
- Muhimman Abubuwa 10 Da Kowa Zai So Ya Sani Game Da Marigayi Shugaban Ƙasa Buhari
“Shugaba Muhammad Buhari babban mutum ne wanda ya yi riƙo da gaskiya da amana da kuma hidimtawa al’ummar Nijeriya” A cewar ƙungiyar gwamnonin.
Kungiyar ta ci gaba da cewa “Tun daga rayuwarsa a matsayin matashin soja da lokacin da ya zama shugaban ƙasa na mulkin soja da na farar hula, Buhari ya kasance mutum mai mutunci da sanin ya kamata. Za a dinga tuna shi wajen sadaukar da kai da rashin son kansa da kuma mayar da hankali wajen aiki ga al’umma da haɗin kan ƙasa da samar da tsaro da ci gaban ƙasarmu”
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana Buhari a matsayin abin koyi musamman ga ƙungiyar gwamnonin Arewa, inda ya bayyana irin tsarin da marigayin yake da shi na gaskiya da yin gwamnati a buɗe.
“A wajenmu ƙungiyar gwamnonin Arewa, Buhari ba iya kawai babban mutum bane a ƙasa, abin koyi ne wanda a ko koyaushe yake tsayawa a kan gaskiya da adalci da kuma riƙon amana. Ya koyar da mutane cikin mutunci , ya yi mulki da ƙwarin gwiwa sannan ya rayu, rayuwa mai sauƙi” in ji gwamnan na Gombe.
Inuwa Yahaya ya ce rasuwar Buhari ta bar gagarumin giɓi wanda kuma za a jima ana jimami.
Tsohon shugaban dai ya rasu ne a yammacin ranar Lahadi a birnin London yana da shekara 82 a duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp