Gwamnatin Jihar Katsina ta ayyana yau Litinin, 14 ga Yuli, 2025 a matsayin ranar hutun aiki da makoki, don girmamawa ga marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.
Buhari, wanda ya kasance shugaban Nijeriya da ya kammala wa’adinsa a baya-bayan nan, ya rasu a ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin Landan, yana da shekaru 82.
Na Yi Rashin Nagartaccen Abokin Aiki, Mai Dattako, Shugaba Buhari —Jonathan
Rasuwar Buhari Babbar Asara Ce Ga Nijeriya — Obasanjo
Sanarwar ta fito cikin wata takarda da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abdullahi Garba Faskari ya sanyawa hannu a madadin Gwamna Dikko Umaru Radda.
A cewar sanarwar, an. Bayar da hutun ne domin bai wa jama dama su yi alhini da kuma addu’o’i neman roƙon rahamar Allah ga rayuwar marigayin.
Gwamna Radda ya bayyana Buhari a matsayin “jagora nagari, gwarzo, ɗan dimokraɗiyya na gaskiya, kuma dattijo mai kishin ƙasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga hidimar Nijeriya.”
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Buhari da al’ummar Jihar Katsina da kuma gabaɗayan ‘yan Nijeriya
“Muna alhinin rashin gwarzon abin koyi kuma wanda ya samu shaidar gaskiya da riƙon amana da kishin ƙasa da sadaukarwa. Muna addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya sanya shi a Aljannatul Firdaus,” cewar Gwamna Radda.
Marigayi Buhari, ɗan asalin Daura ta Jihar Katsina ne, ya shugabanci Nijeriya a matsayin shugaban mulkin soja daga 1983 zuwa 1985 sannan ya dawo a matsayin shugaban ƙasa a mulkin dimokraɗiyya daga 2015 zuwa 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp