• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rawar Da ‘Yan Wasan Afirka Suka Taka A Gasar Premier Ta Ingila

by Abubakar Abba and Sulaiman
1 month ago
in Wasanni
0
Muhammad Salah: Gwarzon Afirka A Firimiyar Ingila
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Tun a cikin watan Mayu aka kammala gasar Premier League ta Ingila, kakar wasa ta 2024 zuwa 2025, inda Mohamed Salah ya taka rawar gani a bajintar da Liberpool ta yi ta lashe kofin gasar kuma aka ayyana danwasan gasar mafi hazaka saboda kwallaye 47 da zira a raga da kuma taimakawa wajen cin 18, adadin da ya sa ya kamo bajintar da tsohon dan wasan Newcastle United, Alan Shearer ya yi a shekarun 1990 da kuma Andy Cole na Manchester United.

Dan kwallon Kamaru Bryan Mbeumo ma ya yi kokari sosai, inda ya ci kwallo 20 da bayar da bakwai a ci – mafi yawa a sana’arsa – kuma ana sa ran zai iya komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United bayan da kociyan kungiyar, Ruben Amorim, ya bayyana dan wasa Mbeumo a matsayin wanda zai taimaka masa wajen ganin ya dawo da kungiyar kan ganiyarta. Ko su wane ne sauran ‘yan Afirkan da suka taka rawar gani a Premier da aka kammala?

  • Diaz Ba Na Sayarwa Bane – Liverpool Ta Fadawa Barcelona
  • Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Kara Habaka Daga Manyan Tsare-Tsare Zuwa Matakai Na Ainihi

Danwasan mai shekara 32 ne kan gaba a jerin mafiya saurin cin ƙwallo mai maki 25.4. Ya buga jimillar shot 130, masu hadari a cikinsu 61,sannan ya taba kwallo a da’irar yadi na 18 ta abokan hamayya sau 394.

Damarmaki 89 da ya kirkira wa abokan wasansa na cikin mafiya a gasar,yayin da Mbeumo ya zo na biyar da damarmaki 70 da ya kirkira a kakar da ta gabata.

Kwallaye 20 da Mbeumo din ya ci kuma sun zarta wadanda aka sa ran zai ci na 12.3. Amma ya hada kai da Yoane Wissa na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo wanda ya ci kwallo 19 shi ma, abin da ya sa zama na biyu mafi kokari cikin ‘yanwasan Afirka na Premier League. Shima dan wasa Antoine.

Labarai Masu Nasaba

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

WAFCON 2025: Yau Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Moroko A Wasan Ƙarshe

Semenyo ma ya taka rawar gani saboda kwallo biyun da ya ci a wasan karshe sun sa ya ci wa kungiyarsa Bournemouth kwallo 11 kenan a karonfarko.

Danwasan Najeriya Aled Iwobi ya fi abokan wasansa kokari a Fulham da kwallayensa tara da ya ci da kuma taimakawa wajen cin shida, sannan ya dan dara Amad Diallo na Manchester United (wanda ya ci takwas kuma ya bayar aka ci shida). Amma Iwobi ya fi shi buga wasanni saboda Diallo ya yi jinyar wajan watanni uku a kakar da ta gabata. Iwobi ne dai kan gaba wajen kirkirar damarmaki (59) da kuma bayar da cikakken fasin (508) a cikin bangaren abokan hamayya, inda shi kuma.

Thomas Partey na Ghana ya fi yawan tura cikakkun fasin (1,631). Shi kuwa Idrissa Gana Gueye ya nuna bajintarsa ne wajen taimka wa Eberton samun damar ci gaba da zama a gasar. Dan Senegal din mai shekara 35 ya cim ma mafi girman bajintar dakatar da abokan hamayya sau 133 kuma ya dauke kwallo daga abokin hamayya sau 221, inda ya zarta kowane dan kwallo daga nahiyar Afrka.

Aaron Wan-Bissaka, shi ne ya fi kowa tare kwallo (66) kuma ya fi yawan yin yanka (64) a ‘yanwasan bayan Premier League – hakan ya sa magoya bayan West Ham suka zabe shi gwarzonsu a bana. Dan Ajeriya Rayan Ait-Nouri, wanda ya koma kungiyar Manchester City a wannan watan ya nuna bajintar kai hari duk da matsayinsa na danwasan baya ta gefe, inda ya ci wa tsohuwar kungiyarsa ta Wolbes kwallo hudu kuma ya bayar aka ci bakwai.

Dan wasa Ola Aina ya taka rawa mafi kyau a tarihi sana’arsa a Nothingham Fores, inda ya dinga kwalo daga ƙafar abokan hamayya sau 190 – mafi yawa kenan da wani danwasan baya ya taba yi. Dan Najeriyar mai buga baya a bangaren dama ya cire kwallo daga kan layin shiga raga sau uku, wanda ‘yanwasa shida ne kawai suka iya yin irin wannan bajintar cikinsu kuma har da Iliman Ndiaye na Senegal.

Calbin Bassey na Najeriya ya taba kwallo sau 2,536 a Fulham – fiye da kowane dankwallon Afirka kenan a gasar – da cikakken fasin 1,926 da ya bayar, da tsige kwallo sau 113, da hana kwallo wucewa sau 17. A gefe guda kuma, Noussair Mazraoui ya tare abokan hamayya sau 115 da kuma dauke kwallo sau 216 daga abokin hamayya a Manchester United.

Andre Onana, mai tsaron raga dan Afirka tilo a Premier League, ya fuskanci kalubale mai girma a kakar bana yayin da Manchester United ta shiga tasku mafi muni cikin shekara 50. Mai tsaron ragar na Kamaru ya buga wasa tara ba tare da an zira masa kwallo a raga ba, amma kuma an ci shi kwallo 44 cikin wasa 25. Hana kwallo shiga raga sau 90 da ya yi shi ne karo na 12 kuma mafiya yawa,

inda adadin ya zama kashi 66 cikin 100 kuma na 15 kenan a tsakanin masu tsaron da suka buga wasa 10 ko fiye da haka. Danwasan mai shekara 29 ya yi kuskure uku da suka jawo zira masa kwallo a raga – ‘yanwasa uku ne kawai suka yi fiye da hakan.

 

Tarihi mara amfani

Danwasan da ya fi kowa yin keta a kakar Premier ta 2024-25 shi ne, Semenyo na Bournemouth, wanda aka busa wa laifi sau 73. Adadin ya zarta na kowane dan wasan Afirka. Samy Morsy na Ipswich Town da kasar Masar, shi ne ya fi kowanne dan Afirka samun katin gargadi (10), sai Gueye da Semenyo da ke da 9 kowanne. An kwace kwallo daga kafar Mohammed Kudus na Ghana da West Ham sau 93, sannan ya buga kwallon da ta daki turke sau shida. Salah da Jackson da Palmer ne kawai suka zarta shi.

Danwasan gaban Chelsea da Senegal Jackson ya yi satar gida fiye da kowa har sau 23. Chris Wood, da Dominic Calbert-Lewin, da Jamie Bardy ne kadai suka kara shi.

Shi kuma dan wasa Taiwo Awoniyi ya fi kowanne dan kwallon Afirka shiga wasa daga baya a Forest, inda Jack Taylor na Ipswich ne kawai ya dara shi zama a bencin. Wasa 23 cikin 26 da dan Najeriyar ya buga ya shiga ne bayan fara wasa.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Wakilin Sin: Matakin Amurka Game Da Harajin Kwastam Bai Yi La’akari Da Rarar Cinikayyar Hidimomi Ba

Next Post

Za A Watsa Shirin “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” A Kafofin Watsa Shirye-shiryen Kasashen Tsakiyar Asiya Biyar

Related

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 
Wasanni

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

7 hours ago
WAFCON 2025: Yau Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Moroko A Wasan Ƙarshe
Wasanni

WAFCON 2025: Yau Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Moroko A Wasan Ƙarshe

18 hours ago
Zan Ci Gaba da Taka Leda A Kano Pillars Duk da Matsayin Da Na Samu — Ahmed Musa
Wasanni

Zan Ci Gaba da Taka Leda A Kano Pillars Duk da Matsayin Da Na Samu — Ahmed Musa

3 days ago
Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Doke Afrika Ta Kudu
Wasanni

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Doke Afrika Ta Kudu

4 days ago
Oshoala Za Ta Yi Ritaya Daga Buga Wa Nijeriya Ƙwallo
Wasanni

Oshoala Za Ta Yi Ritaya Daga Buga Wa Nijeriya Ƙwallo

5 days ago
Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro
Wasanni

Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro

6 days ago
Next Post
Za A Watsa Shirin “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” A Kafofin Watsa Shirye-shiryen Kasashen Tsakiyar Asiya Biyar

Za A Watsa Shirin “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” A Kafofin Watsa Shirye-shiryen Kasashen Tsakiyar Asiya Biyar

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

July 26, 2025
Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

July 26, 2025
Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

July 26, 2025
Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta

Isra’ila Na Sanya Alamar Rusau A Dubban Gidajen Fararen Hula A Gaza

July 26, 2025
Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

July 26, 2025
Afirka

Natijojin Auren Dattijo Ga Budurwa

July 26, 2025
An Yi Bikin Karbar Fitilar Gasar Wasannin Kasa Da Kasa Ta Shekarar 2025 A Chengdu

An Yi Bikin Karbar Fitilar Gasar Wasannin Kasa Da Kasa Ta Shekarar 2025 A Chengdu

July 26, 2025
Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (6)

Dalilan Da Suka Sa Cinikin Bayi Bai Yi Nasara A Arewacin Nijeriya Ba

July 26, 2025
Sin Ta Gudanar Da Gasar Kirkire-kirkire Ta Daliban Kasa Da Kasa A Yankin Afirka Karo Na Farko

Sin Ta Gudanar Da Gasar Kirkire-kirkire Ta Daliban Kasa Da Kasa A Yankin Afirka Karo Na Farko

July 26, 2025
Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson

Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson

July 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.