Kwanakin baya, na ziyarci wani lambun ‘ya’yan itatuwa dake yankin karkarar birnin Beijing na kasar Sin, inda ake yin amfani da na’urorin zamani har nau’ika 28, wajen gudanar da aikin gona.
A baya ana bukatar ma’aikata masu kula da lambun har 60, amma yanzu mutane 6 ne kacal ake bukata, inda suke sarrafa injuna masu gudanar da dukkan ayyuka daban daban.
Shin yawan yin amfani da injuna zai sa manoma su rasa guraben aikin yi? A’a, ba haka ba ne. Wani farfesa mai suna He Xiongkui dake samar da fasahohin zamani ga wannan lambun ‘ya’yan itatuwa ya gaya mana cewa, yanzu haka ci gaban biranen kasar Sin ya sa matasan kauyukan kasar kaura zuwa cikin birane, don neman zaman rayuwa mafi inganci, lamarin da ya haddasa karancin ma’aikata a yankunan karkara.
Don daidaita wannan matsala, dole ne a kara yin amfani da na’urorin zamani wajen gudanar da aikin gona. Wannan dabara ce da kasar Sin ta dauka, a kokarin zamanintar da aikin gona, kana ta nuna wata halayyar musamman ta dabarar raya kasa ta kasar Sin, wato “zabar hanyar da ta dace da yanayin da kasar ke ciki”.
Wannan halayya ta sa hanyar da kasar Sin ke bi a kokarin zamanintar da kai ta sha bamban da ta kasashen yamma, hakan na nuna cewa Sin ba za ta yi koyi da dabarun wasu kasashe na yakar sauran kasashe ba, da yin mulkin mallaka, da kwatar dukiyoyin al’ummun duniya.
A maimakon haka, kasar Sin na tsayawa kan hanyar raya kasa cikin lumana. Idan mun nazarci tarihin Sin, za mu ga cewa, tsakanin shekarar 1840 da ta 1945, bi da bi ne wasu kasashen Turai da ma kasar Japan, suka kai wutar yaki kasar Sin daya bayan daya, lamarin da ya jefa kasar Sin cikin yanayi mai matukar wuya. Kana kasar ta dade ba ta samu farfadowa ba, kafin ta zama cikin wani yanayi na zaman lafiya a shekaru gomai da suka wuce.
Kamar yadda Hausawa kan ce “Kowa ya san ciwon kansa, ya san na wani”. Wannan tarihi na fama da hare-haren da wasu kasashen waje suka kai mata, ya sa kasar Sin zama wata kasar dake iyakacin kokarin tabbatar da zaman lafiya a duniya.
Ban da wannan kuma, tunanin “zabar hanyar raya kasa mai dacewa da yanayin da kasar ke ciki” shi ma ya sa kasar Sin saka buri na baiwa dukkan al’ummun kasar damar samun wadata.
Dalilin da ya sa haka, shi ne tsarin siyasa na Gurguzu na kasar. Wannan tsarin ya sa ana kokarin tabbatar da adalci a zaman al’ummar kasar, da magance karuwar gibi tsakanin al’umma.
Hakika a cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce, hukumar kasar Sin ta fid da kimanin mutane miliyan 800 daga kangin talauci. Wannan jimilla ta shaida kokarin gwamnatin kasar na neman wadatar da dukkan al’ummun ta.
Haka zalika, yadda ake raya kasa bisa yanayin da kasar ke ciki shi ma ya sa kasancewar al’ummar kasar karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta zama dole.
Idan mun waiwayi baya, za mu ga yadda a cikin shekaru fiye da 100 da suka wuce, jam’iyyar ta yi kokarin daidaita matsalolin da kasar ke fuskanta, gami da yi wa kanta kwaskwarima, ta yadda sannu a hankali, kasar ta raya kanta, daga wata kasa mai raunin tattalin arziki, zuwa wata kasar da karfin tattalin arzikinta ya zama na biyu a duniya.
Ta hanyar gudanar da mulki cikin nasara, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ta shaida kwarewarta a fannin yin gyare-gyare, da tsara shiri na dogon lokaci, tare da samun cikakken goyon baya daga jama’ar kasar.
Yadda kasar Sin take la’akari da yanayin kanta, ya sa ta zabar dabarar raya kasa da ta sha bamban da ta kasashen yamma.
Kamar dai yadda Hausawa su kan ce, “Kayan aro ba ya rufe katara”, kana “Ko wace kwarya tana da marufinta”, abun da ya fi muhimmanci, shi ne zabar turba mai dacewa da kai, wadda za ta haifar da hakikanin ci gaban kasa. (Bello Wang)