Jama’a assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a wannan makon. Kafin mu shiga darasinmu na yau, kamar yadda muka yi bayani a game da yanayin cin abinci da baccin Annabi (SAW) a makon da ya wuce, yana da kyau a san cewa, duk hadisai ingatattu da aka ruwaito sun tabbatar da karanta baccin Annabi (SAW). Kuma duk da cewa baccin kadan ne amma sai ga Hadisi yana cewa: “inna ainaiya tanamani, wala yanamu kalbi, idanuna ce kadai take bacci amma zuciyata ba ta bacci.
Amma mu kuma, mu yi bacci ba mu jin komai, shi ne mun yi bacci. Da yawa za ka ji mai bacci yana cewa masu sururtu kusa da kaina duk sun hana ni yin bacci, kuma duk da cewa ya kulle idanuwansa amma (SAW) ya ce shi hakan shi ne baccin shi.
- Mutfwang Ya Amince Da Mafi Karancin Albashi Na N70,000 Ga Ma’aikatan Filato
- EFCC Ta Kwace Fasfon Mataimakin Atiku A Zaɓen 2023
Maganganun da suka gabata, sun yi tsokaci sosai a kan abin da ake son karanta shi kuma ake yabon mai karanta shi “Karanta cin abinci da bacci”. Bari mu yi duba da abunda kuma yabo yake cikin mai yawaita shi.
Wannan bangaren zai yi duba cikin rayuwar Annabi Muhammad (SAW) da abin da ya ta’allaka da aurensa.
Aure al’ada ne kuma addinin mutane ne, mai mata Hudu alfahari yake wurin mai mata uku, mai uku yana kirari wurin mai biyu, mai biyu yana kirari wurin mai daya.
Matsayi ko mukami shi ma abin alfahari ne cikin mutane, ana son yawan mukamai.
Aure, a al’ada da Shari’a duk sun tafi a kan cewa, alama ce ta cikar kamalar mutum da kuma ingancin mazakutarsa. Alfahari da yawaita aure, ta kasance a cikin al’adu a bar alfahari kuma a bar yabo. Aure al’ada ce da ta yadu cikin al’ummatai da Annabawa da Sarakuna. Amma a sunnah, aure sunnar Annabi ce wacce aka ruwaito daga gare shi (SAW).
Abdullahi bin Abbas (Allah ya kara yarda a gare su) ya ce: “Afdalu hazihil ummatu, aksaruha nikahan – mafificin wannan al’umma, shi ne wanda ya fi auratayya. Matan Annabi (SAW) 11, ya rasu ya bar 9, sannan kuma akwai kuyangi.
Annabi (SAW) ya ce “Ku yi aure, ku hayayyafa, ni zan yi alfahari da ku cikin al’ummatai”. Amma fa ga wanda yake da ikon rike su, ba ka da ikon rike daya, ka kwaso biyu, sabida kana so a yi alfahari da kai (wannan ya zama bala’i ba alfahari ba). Amma idan mutum Allah ya hore masa abin ciyarwa da tsaya wa tarbiyyar iyalansa, ba laifi ka auri har mata hudu iyakan karfinka. Yaro ko yarinya daya da za ka iya tsayawa da tarbiyyarta, ta fi masu yawa marasa tarbiyya, don Annabi (SAW) ba za iyi alfahari da maragurbi ba.
Annabi (SAW) ya hana mutum ya yanke cewa, ba zai yi aure ba sabida wani karatu ko zuhudu, amma ba laifi mutum ya ce ina wani aiki yanzun da na kai wani gaba zan yi aure, wannan ba laifi ba ne. Aure yana tumbuke sha’awa, yana sa mutum ya kulle idanunsa daga kalle-kallen matan da ba su halatta a gare shi ba. Sha’awa halitta ce a jikin Dan Adam.
Annabi (SAW) ya ce “Duk wanda yake da halin yin aure, to ya yi, domin aure yana sa mutum ya kulle idanuwansa daga matan jama’a, kuma ya katange ka daga zina”. A wani Hadisin yana cewa “Zinar hannu, shafa; Zinar Ido, gani, Zinar Kafa, zuwa wurin zina; idan aka sadu sun yi gaskiya, idan ba a sadu ba, duk sun yi karya.”
Malamai suna cewa “Yana daga cikin tsantseni mutum ya yi aure.” Masu tsantseni sun fi yawaita aure.
Sahlu bin Abdullahi yana cewa: “su fa mata an soyar da su ga shugaban Halitta Annabi Muhammadu (SAW), ta yaya mutum zai ce zai yi tsantseni a cikinsu”
Malam Dan Uwainata ya ce “Mafi zuhudu, wanda suka yi shuhura cikin Sahabbai (RA), zaka same su sun fi yawan Mata, su ne masu kuyangi.”
Sayyidina Aliyu (Karramallahu wajhahu), shi ne mafi tsantseni cikin sahabbai, an ruwaito cewa, wani bawan Allah ya kawo karar dan’uwansa cewa, Allah Ya azurta shi da dukiya mai yawa amma ba ya amfani da ita, sai Sayyidina Ali ya ce, a kira shi don ya yi masa tambaya, ga abin da ya ce masa “Kai ne a ka ce baka son amfani da dukiyar da Allah ya ba ka?” Sai ya ce “ya Imam, da kai nake koyi!” Sayyidina Ali ya ce, “ni shugaban kasa ne, ina tuna mafi raunin mutanena, shi yasa nake yin hakan. Amma kai ta fi ka yi amfani da abin da Allah ya hore maka, Halal ne a kanka.”
Sayyidina Ali, shine mafi tsantenin sahabbai da zuhudu, wata rana an rahoto cewa, ya yi faci a jikin kayansa, har shi da kansa yana cewa, wannan faci ya yi muni da yawa amma bayan rasuwar Sayyada Fadimatu, an rahoto cewa ya yi auratayya da yawa, yana da ‘ya’ya 31 ban da ‘ya’ya hudu ko biyar na Sayyada Fadimatu. Amma albarka ta zuriyar sayyidina Ali, mafi yawan Ahlul baitin Duniya, zurriyarsa ce.
An rawaito yawan auren Sayyadina Hasan, akwai ruwaya kala-kala kan auratayyarsa, wata ruwaya ya auri Mata 70, wata 90, wata 200, wata 250. Jikan Sayyadina Hasan, Muhammadul Bakeer ya ruwaito cewa Kakansa ya saki Mace 50, amma ikon Allah, duka ‘ya’yansa Maza Da Matan su 24 ne. Amma kuma ikon Allah, wannan zuriya ta Manzon Allah (SAW) da ta cika duniya duk daga Mutum Biyu take kawai: Abdullahil Kamil bin Hasanil musanna da Aliyu Zainul Abidina.
Don haka zuriya a albarka take ba yawansu ba, in Daya Allah ya ba ka, yi masa addu’ar Albarka. Amma in mutum yana da hali, ba a hana shi auratayya ba.
Sayyidina Aliyu Soja ne kuma sarki ne, kowa ya san al’adar sarki, yana samun ganima daga yake-yake da ake yi. Sayyidina Hasan kuma dan Sayyidina Ali ne, kowa yana neman albarkarsa, sannan kuma a kufa ya taso. Wata rana Sayyidina Ali, ya mike cikin garin Kufa yana kira ga mutane cewa, don Allah Jama’a kar wanda ya kara ba wa Hasan Aure, na ji tsoron kar ya jawo min fitina, wani tsoho ya tashi ya ce in ina da ‘ya’ya Mata 100, in ba shi ya saka, in ba shi ya saka, duk sai na ba shi gaba daya. Ba danka ba ne, dan Manzon Allah (SAW) ne, Sayyidina Ali ya ce, ni kuwa da ina da Aljannah da na sa ka.
Abdullahi bin Umar, an ruwaito cewa matansa biyu ne sai kwarkwarori hudu, yana da ‘ya’ya 16.
Idan aka ce ta yaya aure da yawa zai zama cikin abubuwa masu daraja, bayan a Kur’ani Allah yana wa Annabi Yahya Dan Annabi Zakariya’u kirari da cewa “…Sayyidan wahasuran wa nabiyyan minas salihin, Annabi Yahya Shugaba ne, katangagge ne, Annabi ne daga cikin managarta bayi” ta yaya aure da yawa zai zama cikin abubuwa masu daraja? Haka kuma, Annabi Isah (AS), ya koma ga Ubangijinsa ba tare da Aure ba.
Da Maganar kamar yadda ka tabbatar cewa, aure yana daga cikin manyan abubuwan alkhairi da wadannan Annabawan sun yi. Sai malam ya ba wa mai tambaya da amsar cewa: ka sani cewa, kirari da yabo da Allah ya yi wa Annabi Yahya cewa shi katangagge ne (bai taba aure ba) ba kamar yadda wasu masu tafsirai ke fada ba ne cewa, shi gajiyayye ne ba zai iya aure ba ko kuma wai ba ma shi da azzakari ne, a’a , ba haka abun yake ba.
Duk manyan malamai da suka shahara da yin Tafsiri ba haka suka fassara Ayar ba, suka ce, a ce wa Annabin Allah ba ya Aure, wannan tawaya ce kuma hakan bai dace a danganta hakan da Annabawa ba, abin da ayar ke nufi, shi ne, Annabi Yahya katangagge ne daga Zunubi kamar sauran Annabawa, wasu kuma suka fassara da cewa, Annabi Yahya shi ya katange kanshi daga Mata. To wannan zai nuna maka cewa, rashin iko daga yin aure, tawaya ne, amma akwai wadanda suke tumbuke sha’awarsu daga Ibada kamar Annabi Isah da Yahya (AS).
Amma Aure ga wanda Allah ya bashi iko, kuma auren bai tauye masa lokacin Ibada ba, ya tsaya da hakkin auren, to wannan daraja ce, irin wannan darajar ita ce a hakkin Annabinmu (SAW).