Jiya Lahadi 1 ga wata cika shekara daya ne da yarjejeniyar huldar abokantaka ta hadin gwiwar tattalin arzikin shiyya shiyya daga duk fannoni wato RCEP ta fara aiki a hukumance, an lura cewa, yarjejeniyar RCEP ta samar da damammakin cinikayya ga kamfanoni da dama.
A tashar ruwar teku ta birnin Tianjin, wani ma’aikacin kamfanin samar da kayayyakin dake shafar man fetur ya bayyana cewa, “Kayayyakinmu suna kara samun karbuwa a kasar Japan!”. An ga kayayyakin kamfanin sun tashi daga birnin Inchon na kasar Koriya ta kudu domin zuwa birnin Tianjin na kasar Sin, daga baya an jigilar su zuwa kasar Japan ba tare da biyan harajin kwastam ba, wannan ne damar habaka cinikayya da kamfanonin da abin ya shafa suka samu tun bayan da aka fara aiwatar da yarjejeniyar RCEP.
Kungiyar ASEAN ta ba da shawarar daddale yarjejeniyar RCEP ne wadda ke kumshe da kasashen mambobin kungiyar guba goma da kasar Sin da Japan da Koriya ta kudu da kuma New Zealand. RCEP, yarjejeniyar cinikayya maras shinge ne da ta shafi al’ummar kasashe da tattalin arziki da cinikayya mafiya yawa.
A cikin wannan shekarar da ta gabata wato tun bayan da ta fara aiki daga farkon bara, tana aiki ne a kasashe 13 daga cikin 15 wadanda suka daddale yarjejeniyar.
A halin yanzu, tattalin arzikin duniya ya gamu da matsala, don haka ana mayar da yarjejeniyar a matsayin “haske a cikin hazo” wanda zai taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya. Kasar Sin ta shiga yarjejeniyar, lamarin da ya nuna aniyyarta ta kara bude kofa ga ketare.
A nasa bangaren, shigar kasar Sin cikin yarjejeniyar tana da muhimmanci matuka, dalilin haka shi ne tattalin arzikin kasar Sin ya kai kaso kusan 60 bisa dari dake cikin yarjejeniyar, kuma kasar Sin tana samar da sabbin damammaki ga duk duniya bisa sabon ci gabanta. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)