Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na kokarin ganin tsohon dan wasanta da yake buga wasa a kungiyar Al Ittihad ta kasar Saudiyya ya murmure daga raunin da yake fama dashi kamar yadda Al Ittihad ta bayyana.
Benzema ya koma kungiyar dake buga gasar Saudi Pro League a bara bayan shafe shekaru 14 a Santiago Bernabeu, inda ya lashe kofuna da dama da suka hada da gasar Zakarun Turai, Laliga da kuma Super Cup.
Benzema ya sha fama da raunuka tun bayan komawarsa Jedda da taka leda, hakan yasa tsohuwar kungiyarsa ta Real Madrid ta dauki matakin taimaka masa domin samun sauki cikin hanzari, inda aka hada hannu tsakanin likitocin kungiyoyin biyu.