Ƙungiyar Real Madrid ta sake gaza samun nasara a wasan mako na 14 na Laliga da ta tashi 1-1 da Girona a filin Municipal Montilivi a Catalonia, lamarin da ya ƙara tsananta matsin lamba ga tawagar Xabi Alonso. Wannan shi ne karo na uku a jere da Madrid ta kasa cin wasanta, inda ta tattara maki uku kacal daga wasanni uku, duk kuwa da damar da ta ke da ita na komawa saman teburin gasar.
A wasan na Lahadi, Kylian Mbappé ya fara zura ƙwallo amma alƙalin wasa ya soke sakamakon kamun hannunsa da aka gani a VAR. Sai dai a minti na 42 Ounahi ya zura wa Madrid ƙwallo, kafin daga baya Mbappé ya farke sakamakon da bugun fenariti minti na 67. Duk da haka Real Madrid ta nuna rauni a ɓangaren tsaron baya da kuma rashin ƙwarewa a hare-hare.
- El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid
- Atletico Madrid Ta Zazzaga Wa Real Madrid Ƙwallaye 5 A Metropolitano
Sakamakon wannan koma baya ya sauke Madrid daga matsayi na farko zuwa na biyu da maki 33, maki guda kacal a bayan Barcelona da ke kan gaba da maki 34. A wasanninta uku na baya, Madrid ta zura ƙwallaye uku kacal, ta tattara maki uku daga tara da ya kamata ta samu, abin da ke nuna raguwar kuzari yayin da kakar wasannin ke matsowa tsakiya.
Da yake magana bayan wasan, kocin ƙungiyar Xabi Alonso ya ce ba su karaya ba, domin har yanzu akwai sauran dama a gasar. Ya bayyana cewa ƙungiyar za ta lalubo ƙarfinta, ta daidaita salon wasanta, kuma ta sake fafaɗowa da karfi wajen fafutukar lashe Laliga a wannan kakar.














