Kungiyar bada agaji da wayar da kan jama’a ta kasa da kasa, Nigerian Red Cross Society, (NRCS), ta zabi sabbin shugabannin gudanarwarta a Jihar Adamawa.
Zaben shugabannin da za su shugabanci kungiyar na tsawon shekaru hudu, ya gudana ba tare da hamayya ba a harabar asibitin kwararru da ke Yola.
- Za Mu Ci Gaba Da Ayyukan Alheri – Abdulhakeem Kamilu Ado
- Mutum 547,774 Ne Suka Cike Aikin Dan Sanda, Mako 1 Ya Rage Kafin Rufe Shafin Daukar Aikin
Wadanda aka zaban sun hada da Barista Nafisatu Bala a matsayar shugaba, Thomas Ayuba, mataimakin shugaba, Abba Tahir, mai bada shawara kan shari’a, da Injiniya Ari Lutu, ma’ajin kudi kuma mai bada shawara.
Da kuma Jika Abdulhamid, mai bada shawara kan bala’o’i, da Yohanna Hamman Yero Habila, mai tsare-tsare, Muhammed Salihu, mai bada shawara kan kula da lafiya, Ahmed Tijjani Maksha, mai bada shawara kan hanyoyin samun kudade, da Ahmed Babale matasa.
Sauran sun hada da Victoria Taduwukai a matsayar mai bada shawara kan harkokin rabo da ci gaba, Ibrahim Musa Labaran, mai bada shawara kan kwarewa da ayyukan ci gaba, da kuma Usman Suleman Pallam, mai bada taimakon shawara
Da yake rantsar da sabbin shugabannin Mai shari’a Aminu Abdulkadir, ya gargadi shugabannin da su kiyaye ka’ida da aiki da abinda suka rantse akai kamar yadda tsarin kungiyar Red Cross ya tanadar.
Da yake jawabi lokacin rantsarwar shugaban kungiyar ta kasa Prince Oluyemisi Adeaga, ya yaba wa bangaren kungiyar a jihar bisa aikin taimakawa da jinkan da su ke yi wa jama’a, ya kuma bukaci sabbin shugabannin da su dora kan shugabannin da suka gabace su.