• Leadership Hausa
Sunday, December 10, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za Mu Ci Gaba Da Ayyukan Alheri – Abdulhakeem Kamilu Ado

by Abba Ibrahim Wada
3 weeks ago
in Labarai
0
Za Mu Ci Gaba Da Ayyukan Alheri – Abdulhakeem Kamilu Ado
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Wudil da Garko a Majalisar Tarayya, Abdulhakeem Kamilu Ado, ya bayyana cewa za su ci gaba da ayyukan alheri domin ci gaban al’ummar da yake wakilta. 

Mataimaki na musamman ga dan majalisae kan harkokin kafafan yada labarai, Musa Ali Karama ne, ya bayyana hakan.

  • Gwamnan Jihar Filato Zai Garzaya Kotun Ƙoli Don Ƙalubalantar Hukuncin Soke Zaɓensa
  • An Tsinci Gawar Mutum 9 Da Hatsarin Kwale-kwale Ya Rutsa Da Su A Jihar Neje – NSEMA

Ya ce dan majalisar ya yi wannan aiki ne da nufin Allah S.W.A ya kai ladan zuwa kabarin mahaifinsa Marigayi Hon. Kamilu Ado Ajiyan Makaman Kano, wanda ya rasu kwanaki shida kafin zaben 2023.

Aikin, wanda aka yi kwanaki uku ana yi an kammala ne a ranar Lahadi 19 ga watan Nuwamba 2023, inda aka yi wa kimanin sama da mutum dubu 1500.

La’akari da muhimmancin da ido yake da shi a jikin dan Adam ya sa dan majalisar ya dauki nauyin yin aikin kyauta a babban asibitin Wudil.

Labarai Masu Nasaba

Sojojin Somaliya Sun Kashe Mayakan Al-Shabab 60 A Yankin Tsakiyar Kasar

Mali Da Nijar Za Su Kawo Karshen Yarjejeniyar Haraji Da Faransa

Kazalika, an yi wa al’ummar Karamar Hukumar Garko a asibitin cikin garin Garko, wanda aka kwashe tsawon kwanaki uku ana gudanarwa.

Wasu daga cikin al’ummar da aka yi wa aikin sun amfana da gilashi da magunguna yayin da wasu kuma aka yi musu aikin tare da basu magunguna duk a kyauta.

Har ila yau, wasu daga cikin makwabtan kananan hukumomin Wudil da Garko su ma sun amfana da wannan tallafi, duk da ba ‘yan kananan hukumomin ba ne.

A karshe, Hon. Abdulhakeem Kamilu Ado ya yi kira ga majinyatan da su kasance masu bin ka’idojin da likitoci suka gindaya musu don tabbatar da samun cikakkiyar lafiyar idanunsu, tare da fatan samun sauki

Tags: Abdulhakeem Kamilu AdoAikin IdoAsibitiDan MajalisaWudil
ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamnan Jihar Filato Zai Garzaya Kotun Ƙoli Don Ƙalubalantar Hukuncin Soke Zaɓensa

Next Post

Gavi Ya Samu Mummunan Rauni A Tawagar Spaniya

Related

Sojojin somaliya
Labarai

Sojojin Somaliya Sun Kashe Mayakan Al-Shabab 60 A Yankin Tsakiyar Kasar

4 hours ago
Faransa
Labarai

Mali Da Nijar Za Su Kawo Karshen Yarjejeniyar Haraji Da Faransa

6 hours ago
Yobe: Za A Rataye Sojan Da Ya Harbe Malamin Addini
Labarai

Yobe: Za A Rataye Sojan Da Ya Harbe Malamin Addini

15 hours ago
Tsaro: Yadda Sojoji Ke Rakiyar Matafiya Tsakanin Gusau Zuwa Dansadau
Labarai

Tsaro: Yadda Sojoji Ke Rakiyar Matafiya Tsakanin Gusau Zuwa Dansadau

15 hours ago
Gwamnatin Katsina
Labarai

Gwamnatin Katsina Ta Kara Jaddada Matsayinta Kan Bunkasa Ilimi

1 day ago
Zakka
Labarai

An Bukaci Gwamnatin Kaduna  Ta Samar Da Hukumar Zakka Da Wakafi

1 day ago
Next Post
Gavi Ya Samu Mummunan Rauni A Tawagar Spaniya

Gavi Ya Samu Mummunan Rauni A Tawagar Spaniya

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya

Nijeriya Ta Koma Ta 44 A Fagen Kwallon Kafa A Duniya

December 10, 2023
City

Ana Tuhumar Manchester City Da Laifin Rashin Tarbiyya

December 10, 2023
Sojojin somaliya

Sojojin Somaliya Sun Kashe Mayakan Al-Shabab 60 A Yankin Tsakiyar Kasar

December 10, 2023
Gwamna Yusuf

Gabatowar Kidaya: Jan Hankali Ga Jama’ar Kano

December 10, 2023
Faransa

Mali Da Nijar Za Su Kawo Karshen Yarjejeniyar Haraji Da Faransa

December 10, 2023
Tsohon Firaministan Austria: Ra’ayin “Raba Gari Ta Fannin Tattalin Arziki” Bai Dace Ba

Tsohon Firaministan Austria: Ra’ayin “Raba Gari Ta Fannin Tattalin Arziki” Bai Dace Ba

December 10, 2023
Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Kin Amincewar Amurka Da Kudurin Tsagaita Wuta Domin Jin Kai

Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Kin Amincewar Amurka Da Kudurin Tsagaita Wuta Domin Jin Kai

December 10, 2023
Yadda Kasar Sin Ke Ba Da Gudummawar Tinkarar Sauyin Yanayi A Duniya

Yadda Kasar Sin Ke Ba Da Gudummawar Tinkarar Sauyin Yanayi A Duniya

December 10, 2023
Yobe: Za A Rataye Sojan Da Ya Harbe Malamin Addini

Yobe: Za A Rataye Sojan Da Ya Harbe Malamin Addini

December 9, 2023
Tsaro: Yadda Sojoji Ke Rakiyar Matafiya Tsakanin Gusau Zuwa Dansadau

Tsaro: Yadda Sojoji Ke Rakiyar Matafiya Tsakanin Gusau Zuwa Dansadau

December 9, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.