Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, Nana Kashim Shettima, da matan gwamnonin jihohi sun bayar da gudunmawar Naira miliyan 500 don tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da kewaye.
A wata ziyarar jaje da ta kai wa Gwamna Babagana Zulum a ranar Laraba a gidan gwamnati da ke Maiduguri, Uwargidan Shugaba Tinubu wacce Nana Shettima ta wakilta, ta bayyana jimaminta kan yadda ambaliyar ruwa ta mamaye garin, inda ta bayyana hakan a matsayin “ikon Allah ne kadai”.
- Za A ‘Yantar Da Falasɗinawa Nan Ba Da Jimawa Ba – Fani-Kayode
- Dakta Gadan-ƙaya Ya Bada Haƙuri Kan Zargin Auren Jinsi Da Ya Yi A Bauchi
“Ina jajantawa Gwamna Babagana Umara Zulum da al’ummar Borno, Allah ne kadai zai iya saka wa mutane asarar da suka yi.” Inji ta.
Tawagar da ta hada da uwargidan mataimakin shugaban majalisar dattawa da kuma uwargidan gwamnan jihar Legas ta samu tarba daga gwamna Zulum.
Ta mika jajenta, inda ta ce, “A matsayinmu na Musulmi, mun gode wa Allah, mun san duk abin da ya faru daga gare shi ne,” ta yi addu’ar Allah ya kawo mana dauki, ya kare afkuwar ambaliyar ruwan a nan gaba.
Tawagar ta kuma kai ziyarar jaje ga Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Garbai Al-amin Elkanemi inda suka jajanta wa Sarkin bisa ambaliyar ruwa da ta mamaye fadarsa.