Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya gana da manyan hafsoshin tsaro da shugabannin hukumomin leƙen asiri na Najeriya kan kalaman shugaban Amurka, Donald Trump.
Trump ya yi iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci a Nijeriya, yana mai cewa idan gwamnatin Nkjeriya ba ta ɗauki mataki cikin gaggawa ba, zai iya turo sojojin Amurka domin yaƙar waɗanda ya kira da “’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi.”
- Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
 - “Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan Trump
 
A wata sanarwa da ya fitar, Trump ya ce, “Na bayar da umarni a fara shirin ɗaukar mataki.
“Idan har za mu kai hari, za mu yi hakan cikin gaggawa, ba tare da ɓata lokaci ba, kamar yadda waɗannan ‘yan ta’adda ke kai hare-hare kan Kiristoci.”
Sai dai gwamnatin tarayya ta yi martani ta bakin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa babu wata barazana da Kiristoci ke fuskanta a ƙasar.
Ya jaddada cewa gwamnati tana tabbatar da tsaron kowa ba tare da bambanci ba.
Kalaman Trump sun haifar da ruɗani da cece-ku-ce a tsakanin ‘yan Nijeriya.
			




							








