ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ribadu Ya Kara Jaddada Gargadinsa Kan Biyan Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane

by Sulaiman
7 months ago
Ribadu

Babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya kara jaddada gargadinsa kan ci gaba da biyan kudaden fansa ga masu garkuwa da mutane, duk da wasu na ganin hakan a matsayin sauki garesu amma illa ne sosai.

Ribadu ya yi gargadin ne a lokacin da ya amshi sabbin mutane 60 da aka sako daga hannun masu garkuwan, biyo bayan azama da sojoji suka sanya a Jihar Kaduna.

  • Ministan Tsaro Ya Yi Gargadin Sake Dawowar Boko Haram Na Barazana Ga Nijeriya
  • Kasar Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Mai Samar Da Sadarwar Intanet

Daga cikin wadanda aka sako har da mataimakin daraktan a ma’aikatar gwamanti da kuma dan uwan Bishop Matthew Hassan Kukah, wadanda dukkanin suka fito daga Zango Kataf da ke kudancin Kaduna.

ADVERTISEMENT

A cewar Ribadu, biyan kudin fansa shi ke kara rura wutar garkuwa da mutane kuma shi ne ke kara wa masu garkuwan karfi, don haka daina ba su zai taimaka wajen rage musu satar mutane.

“Bari na roki mutanenmu, iyalai da su daina bai wa ‘yan ta’adda kudade. Don Allah a daina ba su kudade. Kudin da kuke ba su na kara rura matsalar. Ba mu taba bai wa wadannan mutane kudin. Bai wa wadanda sheidanun kudade shi ne ke kara ba su damar satar wasu a gaba. Yawan kudin da kuke ba su, yawan kara neman kudin da suke yi,” ya shaida.

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Wani rahoton tsaro da hukumar Kididdiga (NBS) ta fitar a watan Disamban 2024, ta ce, yawan kudin fansa da jama’an Nijeriya suka biya ya zarce naira tiriliyan 2.23 ga masu garkuwa da mutane daga Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024.

A cewar rahoton na CESPS, kusan kashi 65 cikin 100 na magidanta da suka fuskanci matsalar sace-sacen jama’a sun biya matsakaitan kudin fansa na naira miliyan 2.67, wanda ya kai naira tiriliyan 2.23.

An fitar da rahoton ne kwana guda bayan rahoton hukumar kare kakkin Dan’adam na Nijeriya na shekarar 2024, ya nuna cewa akalla mutane 526 ne aka kashe a wasu munanan hare-hare tare da yin garkuwa da wasu 949 a wasu sassan kasar.

Duk da masana sun sha nusar da jama’a illar biyan kudaden fansa ga ‘yan fashin daji, mutane ko iyalai suna ganin biyan kudin shi ne mafita a garesu a duk lokacin da aka sace musu wani nasu, lamarin da ke kara nuna sakacin jami’an tsaro, a cewar mutane da dama in ba su biya kudin fansar ba suna iya rasa dan uwan nasu da aka sace.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Next Post
Ministan Harkokin Wajen Sin Zai Halarci Taron Ministocin Kula Da Matakan Taron FOCAC Da Bikin Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Afirka Karo Na 4

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.