Wani rahoto da hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar a yau Litinin ya nuna cewa, ribar da manyan masana’antun kasar Sin suka samu cikin watanni tara na farkon shekarar 2025 da muke ciki, ta karu da kashi 3.2 cikin dari.
A cewar hukumar ta NBS, masana’antun da ke samun kudaden shiga da suka kai akalla yuan miliyan 20 (kimanin dala miliyan 2.8) a shekara-shekara, sun samu jimillar ribar da ta kai yuan tiriliyan 5.37 a cikin watanni taran.
A watan Satumba, ribar da manyan masana’antun ke samu ta farfado sosai, inda ta karu da kashi 21.6 cikin dari a kan na makamancin lokacin a bara, kamar yadda hukumar ta NBS ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














