Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS ta fitar a yau Asabar sun nuna cewa, yawan ribar da manyan kamfanonin masana’antu na kasar Sin suka samu ya karu da kashi 3.5 cikin dari a cikin watanni shida na farkon bana idan aka kwatanta da makamancin lokacin na bara.
Yawan ya karu ne daga kashi 3.4 cikin 100 da aka samu a watanni biyar na farkon shekarar. (Mai fassara: Yahaya)