Alkaluma daga hukumar kididdiga ta kasar Sin sun bayyana cewa, daga watan Janairu zuwa na Maris a bana, yawan ribar da kamfanonin masana’antun dake iya samun kudin shiga da yawansa ya zarce dalar Amurka miliyan 2.74 a kowace shekara, ya wuce dalar Amurka biliyan 207.1, wanda ya karu da 0.8% bisa na makamancin lokaci a bara. Hakan ya bayyana daina raguwar alkaluman a wannan bangare.
Hukumar ta kara da cewa, a wadancan lokuta, yawan ribar da aka samu a wannan bangare ya samu karuwar 0.8% daga raguwa na 3.3%. A watan Maris da ya shude kuma, ribar da kamfanonin suka samu ya karu da 2.6%, matakin da ya canja halin da aka shiga a watannin Janairu da Fabrairu na raguwa da 0.3%.
- Me Ke Sa Amare Yin Watsi Da Kwalliya Idan Sun Kwana Biyu A Gidan Miji?
- Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje
Ban da wannan, kamfanonin masu sana’o’in da yawansu ya kai kusan 60% sun samu karuwar riba, musamman ma masu sana’o’in samar da kayayyaki. A wadancan lokuta, a cikin kamfanonin masu sana’o’i 41, masu sana’o’i 24 sun samu karuwar riba bisa na makamancin lokacin bara, adadinsu da ya kai kimanin 60%, kana masu sana’o’i 24 sun fi samun saurin karuwar riba ko kuma raguwar raguwar riba daga watan Janairu zuwa na Fabrairu, yawansu da ya kai 58.5%.
Bugu da kari, an fi samun kyautatuwa a bangaren samar da kayayyaki, inda yawan ribar da aka samu a farkon watanni 3 na bana ya karu da 7.6%, saurin karuwar ya kai 2.8%. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp