Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Similanayi Fubara, ya bar Gidan Gwamnati da ke Fatakwal.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa ya fice daga gidan ne da safiyar Laraba, yayin da sabon Shugaban Riƙo, Admiral Ekwe Ibas (mai ritaya), ke shirin karɓar mulki.
- Za Mu Bi Doka Domin Dawo Da Haƙƙinmu – Fubara
- ’Yan Banga Sun Ceto Mutum 3 Daga Hannun ’Yan Bindiga A Taraba
Rahotanni sun nuna cewar an samu kwanciyar hankali duk da zaman ɗari-ɗari da ake yi tun jiya.
Motocin yaƙi guda uku na sintiri a bakin Gidan Gwamnatin jihar.
Wani jami’in tsaro ya tabbatar da cewa an sauya duka jami’an tsaro da ke Gidan Gwamnati da wasu sabbi.
“Gwamna ya fice daga gidan, kuma muna jiran sabon shugaban riko ya iso.
“An sauya duka jami’an tsaro, amma komai yana tafiya cikin kwanciyar hankali a yanzu,” in ji majiyar.
A halin yanzu, al’ummar Fatakwal na ci gaba da harkokinsu ba tare da wata matsala ba.
A ranar Talata ne, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ayyana Dokar Ta-ɓaci a Jihar Ribas, sakamakon rikicin siyasa da addabi jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp