Ƴan ta’addan Boko Haram sun kashe masunta 18, a wani harin da suka kai a yankin Mobbar, wanda ke arewacin Jihar Borno, kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar. Harin ya faru ne a kogin Fadana-Garuwa a yankin Duji, lokacin da mayakan suka kai hari cikin ruwan, inda suka zargi masu kamun kifin da haɗin kai da ‘yan ta’addan ISWAP.
A cewar wani mai kamun kifi da ya yi magana da wakilinmu, Boko Haram sun zo da yawan gaske suka yi ta kai hari kan masu kamun kifin, suna zargin su da kai rahoton maɓoyarsu ga ‘yan ta’addan ISWAP. Sun tattara su duka, suka kashe su, sannan suka yi barazanar cewa wannan hukunci ne ga wanda ke aiki tare da ISWAP.
- Mayaƙan ISWAP Da Boko Haram 4 Sun Tuba Sun Miƙa Wuya A Borno
- Talauci Da Rashin Ilimi Ne Ya Sa Ayyukan Boko Haram Ke Dawowa – Gwamnan Yobe
An tabbatar da cewa yankin na cikin ikon Boko Haram da sauran ruwan da ke kusa da iyakar Nijar, kuma wannan hari yana da alaƙa da rikicin dake tsakanin bangarorin Boko Haram da ISWAP. An samu gawarwakin mutanen 18, yayin da wasu da dama suka bace. Tuni al’ummar yankin suka gudanar da jana’izar su bisa tsarin Musulunci.
A cikin watannin da suka gabata, duka ɓangarorin Boko Haram da ISWAP sun ƙara yawan hare-haren su kan fararen hula da sansanin Soja a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa, wanda ya haifar da ƙarin tashe-tashen hankula a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp