Idan muka duba rikicin cikin gida na jam’iyyun siyasa yana samun asali ne kan yadda ake tafiyar da ita siyasar a tsakanin shugabanninta. Bari mu fara da jam’iyyar APC da take rike da mulkin kasa da kuma Jihohi masu rinjaye.
Dole ne rikici ya rika tasowa lokaci zuwa lokaci wannan kuma hakane rayuwa ta gada domin ba kullum bane ake kwana gado ba.
Mutum ya kamata ace ya saba da hakan kamar dai yadda harshe da hakori ma watarana ana dan batawa, kuma abin ba a jin dadi ko kadan da akwai wuya. Akwai abubuwa da yawa da su kan faru a jam’iyya wadanda ba a sanin su domin ba a bari har su kai ga fitowa fili har wasu su kai ga jin irin halin da ake ciki.
Kamar dai abinda ya faru a jam’iyyar APC wanda bayan da aka yi zaben fidda gwani na jam’iyyar ne a ranar 8 ga watan Yuni 2022, cikin wannan makon ne abin boye ya fito fili, ashe an bata ma wasu rai a jam’iyyar amma suna nan ba za su fita ba, ba za su bar ta ba.
Ko shakka babu tsohon gwamnan Jihar Ribas har ila yau kuma tsohon Ministan Sufuri Chibuke Rotimi Amechi, ya b ada gaggarumar gudunmawa a jam’iyyar APC.
Tunlokacin da ya dawo jam’iyyar cikinta tare da tsohon gwmnanJihar Kwara tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki. Shi ma tsohon shugaban majalisar wakilai ta tarayyya Aminu Waziri Tambuwal tare da har ila yau tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar haka suka baro wurin da ake taron PDP suka zarce zuwa dakin taro na ‘Yar’adua Centre inda daga can suka bada labarin ficewarsu daga jam’iyyar.
Kafin ya dawo jam’iyyar APC lokacin yana PDP ba karamar gwagwarmaya ya yi da shan wahala cikin Jihar ta su ta Ribas ba, da ma sashen na Kudu maso Kudu gaba daya, amma duk da hakan ya yi hakuri da ci gaba da zama a jam’iyyar.
Lokacinzaben fidda gwani na jam’iyyar APC shi ya kasance na biyu wanda yake bin Sanata Bola Ahmed Tinubu da ya kasance dan takarar jam’iyyar, mataimakin Shugaban kasa Farfesa Osinbajo ya zama na uku.
Komai aka fada kan Amechi ba zai isa ba kan gudunmawar da yake ci gaba da ba jam’iyyar APC.Har zuwa lokacin da aka bayyana sunayen wadanda za su taimaka wajen yakin neman zabe na dan takarar jam’iyyar APC na dukkan mukaman ba a ji an ambaci sunan sa ba.
Wike kamar Amechi dan Jihar Ribas ne amma shi dan jam’iyyar PDP ne yana ta bata gudunmawa wajen tafiyar da ita, domin ba gamawa ya yi ba.
Idan dai jama’a ba mantawa suka yi ba lokacin da jam’iyyar ta shiga cikin babban rikicin Shugabancinta daga karshe sai da Uche Sokondus Shugaban jam’iyyar na lokacin ya sauka.
Bayan an yi zaben da ya samar da Sanata Iyorchia Ayu a matsayin Shugaban jam’iyyar, sai bayan da aka yi zaben fidda gwani ne na jam’iyyar PDP. Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya zama dantakarar Shugaban kasa na jam’iyyar.
Kamar dai yadda aka saba sai abin ya zama kamar ‘yan tagwaye shi ma Wike ya zo na biyu kamar dai Amechi shi ma haka ya kasance sai ba a jawo shi a jiki ba. Maimakon haka ma sai aka mai da shi saniyar ware, kamar dai yadda aka yi ma tsohon Ministan Sufuri Chibuke Rotimi Amechi aka mai da Garma da aka shekara aiki da ita amma aka barta tsirara.
Tun lokacin da aka kammala zaben fidda gwani na jam’iyyar, ba a faye jin duriyarsa ba,bai yin magana kan wani al’amari shi ma, ba,a yin maganar data shafe shi.
Irin hakan ne ya sa yanzu ya zame masu Kadangaren bakin Tulu a kashe shi a kar Tulun idan kuma aka bar shi ya bata ruwan.Ya tada ma jam’iyyar hankali har zuwa yanzu abubuwa a kudundune suke suna tafiyar Hawainiya, domin kuwa bayan kwamitocin da aka kafa biyu sun kasa zama.
Dagakarshe ma har Atiku da Wike suka hadu a London suka yi kwalli da juna amma abin har yanzu da sauran rina a Kaba.Shi ma bai ce zai bar jam’iyyar ba,sai dai ya yi mata wani jirwaye mai kamar wanka inda yace zai taimaka mata ta fadi zabe.
Matsawa da maganganun da Wike ya ci gaba da yi ta sa har Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar Sanata Wali Jibril ya sauka daga kan mukaminsa.Amma har yanzu Wike bai amince da hakan ba so yake Ayu ya sauka daga jagorancin jam’iyyar gaba daya, watakila idan da an ba shi mataimakin dantakarar Shugaban kasa na jam’iyyar da tuni an wuce wurin da ake yanzu.
Amma babu wani abu kwakkwara da aka yi ma shi watakila shi yasa har yanzu hankalinsa ba kwanciya ya yi ba, me yiyuwa ne har sai lokacin da yaga Ayu ya yada kwallon Mangwaro domin ya huta da Kuda.
Ba Amechi da Wike kadai ba ne aka taba bata ma rai a siyasance ba idan aka yi la’akari da yadda siyasar take tafiya halin da ake ciki yanzu, sai dai mutanen biyu wadanda ana iya cewa sun zama tamkar tagwaye ne a wasu abubuwa sun dai dan bambanta ne. Suna cikin shan gwagwarmayar siyasa domin ai ba gamawa suka yi ba, suna yi ma siyasar aiki tukuru matuka sai dai har yanzu hakarsu bata kai ga cimma ruwa ba tukunna.
Amechi ya bar jam’iyyar PDP ya koma ta APC sai dai shi kuma Wike har yanzu yana nan a PDP bai taba barinta ya koma ma wata jam’iyya ba. An kuma san gwarzon yin ayyukan ci gaban al’ummar shi ne.