Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa da ƴan Nijeriya cewa za a ci gaba da samun isasshen man fetur duk da barazanar shiga yajin aiki da ƙungiyar PENGASSAN ta yi kan taƙaddama da matatar man Dangote. Wannan na zuwa ne bayan raɗe-raɗin cewa matatar ta dakatar da tsarin siyar da ɗanyen mai da ake biya sa da Naira.
A wata sanarwa daga ma’aikatar kuɗi ta tarayya, daraktan hulɗa da jama’a Mohammed Manga ya bayyana cewa an gudanar da taron kwamitin kula da tsarin “buyqn Naira-don sayen ɗanyen mai” ƙarƙashin jagorancin Ministan Kuɗi, Wale Edun. Taron ya samu halartar Ministan tsare-tsare, da shugaban FIRS, da wakilai daga NNPC, CBN, NMDPRA da Afreximbank.
- Matatar Dangote Ta Dawo Sayar Da Man Fetur A Kuɗin Naira
- Ana Hasashen Tashin Fetur Idan Matatar Dangote Ta Daina Karɓar Naira
Sanarwar ta bayyana cewa matatar Dangote ta tabbatar ba za a samu tangarɗa ba wajen samar da man fetur, tare da jaddada cewa tsarin biyan Naira zai ci gaba da aiki yadda aka tsara. Haka kuma, an tabbatar cewa Ƙorafe-ƙorafen PENGASSAN na cikin abubuwan da za a bincika kuma a tattauna
Gwamnati ta ce tana ɗaukar matakan gaggawa cikin gaskiya wajen warware duk wani saɓani domin kare kowanne tsagi, da tabbatar da tsaron makamashi, da kiyaye daidaito a kasuwar man fetur. An kuma yi kira ga ƴan ƙasa da su kwantar da hankalinsu yayin da ake ci gaba da shawo kan batun.