Majalisar Dattawa ta kasa ta amince da kudirin neman diyya ga wadanda zanga-zangar EndSARS ta shafa, a karatu na biyu.
Kudirin, wanda Sanata Gershom Bassey (PDP, Cross River) ya jagoranta, ya tsallake matakin karatu na biyun ne a zauren majalisar a ranar Laraba.
In ba a manta ba, a watan Oktoban 2020, an gudanar da wata gagarumar zanga-zangar lumana ta neman dakatar da ‘yansandan SARS, wacce daga bisani ‘yan sara-suka suka juya akalar zanga-zangar ta koma tashin hankula da kone-konen dukiyoyin jama’a da basuji ba au gani ba kuma tayi sanadin rasa rayukan wasu jami’an ‘yansanda a Jihar Legas.
Da yake jagorantar muhawarar kan ka’idojin kudurin, Sanata Bassey ya ce koken da ya gabatar na neman samar da asusun biyan diyya ga wadanda aka kashe a yayin zanga-zangar ta EndSARS.
Bayan muhawarar, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, daga baya ya mika kudirin ga kwamitin ayyuka na musamman na majalisar don duba kudurin a tsarin kundun majalisa acikin mako guda.