A karo na farko Hamas ta harba makamai masu linzami kan filin jirgin sama na ‘Ben Gurion airport’ da ke birnin Tel Avib babban birnin kasa Isra’la.
A birnin San Francisco na Amurka kuwa dubban mutane suka yi zanga zangar goyon bayan Falasdinawa, da kuma la’antar Israila.
Kawo yanzu yahudawa 2,382 suna kwance hajaran majaran cikin munanan raunuka, wasu na ma na iya mutuwa a koda yaushe.
Israila ta sanar da cewar an sake kashe mata sojoji 16 a bakin daga, amma kafofin Falastinawa sun bayyana cewar lamarin ya linka hakan sosai.
- Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Yi Taro Kan Rikicin Isra’ila da Falasdinu
- Rikicin Falasdinu Da Isra’ila: Saudiyya Ta Dakatar Da Duk Wata Tattaunawa Da Isra’ila
Israila ta sanar da cewar yahudawan da suka mutu sun kai mutun 1,030. Anadolu News Agency sun tabbatar da hakan.
Kafofin sadarwar Israila sun bayyana cewar yahudawan da ke Hannun Hamas sun kai mutum 150. Hamas ta ce cikinsu mutum 100 duk sojoji ne har da manyan jami’an sojan yahudu.
Hukumomin lafiya a Falastinu sun sanar da cewar Falastinawa 456 suka yi shahda, a cikinsu akwai yara 78 sai mata 46. Tashar Aljazeera ta tabbatar da hakan.
Shugaban kungiyar HAMAS Ismail Abu Haniye ya tattauna da shugaban kasar Iran, ya yi masa karin haske kan halin ďa ake ciki. Ya yi wa shugaban da kuma al’ummar Iran godiya bisa gòyon bayan da suke bai wa Falastinawa.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi zaman sirri kan yakin amma har yanzu sun kasa cimma matsaya daya, ana sa ran za su ci gaba da zaman domin ganin abin da zai yiwu.
Bayanai sun nuna cewa, adadin mamata na karuwa a tsakanin dakarun Hamas da na Isra’ila a Gaza, Isra’ila ta sake karbe iko da yankunan kan iyakar Zirin Gaza, a yayin da adadin wadanda suka mutu a bangarorin biyu ke ci gaba da karuwa, sakamakon rikicin da ya barke, biyo bayan wani mummunan harin da kungiyar Hamas ta kaddamar kan yankunan da Israila ta mamaye , wanda ba a taba ganin irinsa ba.
A yayin da Isra’ila ta zafafa hare-haren sojinta kan yankin Zirin Gaza, an jiyo wani kakakin ma’aikatar tsaron kasar, Laftanar Kanar Jonathan Conricus na cewa, yawan adadin rayukan mutanen da suka salwanta a bangaren Yahudawan ya kai dubu 1.200
Ya ce Isra’ila ta jibge dakaru dubu dari 300 a kusa da yankin Zirin Gaza, wadanda ke a shirye don aiwatar da umurnin da gwamnatin kasar ta ba su.
A bangaren Falasdinawa kuma, ma’aikatar kiyon lafiyar yankin Zirin Gaza ta ce, adadin wadanda suka mutu ya haura mutane dari 900, a yayin da hare-haren da Isra’ila ke kai wa yankin ke ci ga da kamari.
Kamfanin da ke samar da wutar lantarki a yankin na Gaza da ke kunshe da yawan al’umma sama da miliyan 2, ya ce, wutar lantarki na iya daukewa nan da ‘yan sa’o’i, sakamakon karancin makamashin da tashar samar da wutar fama dashi.
Zirin-Gaza ya yi ta fama da daukewar wutar lantarki tun bayan harin da kungiyar HAMAS ta kai cikin yankunan da Isra’ila ta mamaye, sakamakon luguden wuta da dakarun na Isra’ila su ke ta yi babu kakkautawa kan yankin na Gaza tun safiyar ranar Asabar da ta gabata, abin da ya sa hatta asibitoci a mafi yawan lokuta, ke gudanar da ayuka cikin duhu ba tare da wutar lantarki ba.
Kasashe da al’ummar duniya suna ta kiraye-kiraye ga bangarorin biyu da su kai zuciya nesa su stakaita wuta don rage kuncin da al’umma suka shiga a yankunan biyu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp