Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana cewa bisa kididdiga, fiye da daliban Nijeriya 99,985 suka arce zuwa jami’o’in kasar Ingila a tsakanin 2017 zuwa 2022.
Ministan ya bayyana hakan ne a jawabisa lokacin bude taron bikin jami’ar Legas ta 2023 a ranar Litinin a Jihar Legas.
- Tinubu Ya Nada Olukoyede A Matsayin Sabon Shugaban EFCC
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Muhimmanta ‘Yancin ‘Yan Jarida – Minista
“A duk shekara sama da daliban Nijeriya 100 suke amfana da tallafin karatu na digiri na biyu da kuma digiri na uku, na yi magana da daliban da kaina, muna da daruruwan kwararru da ‘yan kasuwa da suke barin kasar nan zuwa kasashen ketare.
“A bangarenmu, dole ne mutabbatar da cewa mun taka muhimmiyar rawa wajen ganin sun cimma burikansu. Sun dauke tambarin kasarmu kuma ba wai suna zuwa taimako ba ne, sai dai domin su sayar da kansu.
“Bisa kididdigar rahoton manyan makarantu ya nuna cewa sama da daliban Nijeriya 99,985 suka bar kasar nan, inda suka arce zuwa jami’o’in kasar Ingila a tsakanin 2017 zuwa 2022.
“A yayin da dimbin wadannan dalibai suka fice ba tare da wani dalili ba, ba za mu iya gasgata cewa yawan wadannan dalibai sun bar kasar domin karo ilimi ba ne ko kuma sun ce sayar da kan su.
“Bisa wannan lamari, a nan zan yi tambaya, me ya sa dalibanmu suke shan wahala wajen samun fasfo ko da ake sun biya kudi.
“Snuna fuskantar sabbin kalubale a iyakoki, madadin a ce ana ba yaranmu jindadin da ya kamata damin su cimma burikansu,” in ji shi.
Ministan ya kara da cewa ma’aikatarsa ta samar da kawo karshen wahalar samun fasfo na bayar da wa’adi ta yadda ‘yan Nijeriya za su samu cikin sauki.