Adadin wadanda suka rasu sakamakon barkewar rikici tsakanin Isra’ila da Hamas ya kusan 1,000 inda aka kashe Isra’ilawa sama da 600 da Falasdinawa 370 ya zuwa yanzu.
LEADERSHIP ta bayar da rahoton cewa, fadan ya barke ne bayan da wata kungiyar Hamas ta Falasdinawa, ta kai wa Isra’ila hari a ranar Asabar inda ta harba makamin roka da yawa daga zirin gaza wanda da farko ya kashe Isra’ilawa 22.
- Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Kira Da A Tsagaita Wuta A Rikicin Isra’ila Da Hamas
- Sin Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jirage Marasa Matuka Da Aka Kai Kan Wata Makarantar Soji A Syria
Sakamakon haka, Isra’ila ta mayar da martani kamar yadda firaminista Benjamin Netanyahu ya sha alwashin, yana mai cewa: “Makiyanmu za su dandana kudarsu. Mun kaddamar da yaki da Falasdinu kuma mu za mu yi Nasara”
Gwamnatin Isra’ila ta fada a yammacin ranar Lahadi cewa, an kashe Isra’ilawa sama da 600 tare da yin garkuwa da 100 a hare-haren da aka kai daga Gaza tun ranar Asabar.
Ya kara da cewa, sama da 2,000 sun jikkata.
Kazalika, bangaren jami’an Falasdinawa sun ce, harin ramuwar gayya da IsrIsra’i kai, ya kashe mutane akalla 370 a zirin Gaza, tare da jikkata wasu 2,200.