Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi kira da a tsagaita wuta a rikicin da ya kaure a tsakanin Isra’ila da Hamas.
A wata sanarwa da ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ya fitar, ya ce, gwamnatin ta damu matuka game da barkewar rikicin da ya barke da sanyin safiyar ranar Asabar.
- NDLEA Ta Cafke Wani Tsoho Mai Shekaru 67 Dauke Da Hodar Ibilis A Filin Jirgin Saman Abuja
- “Makon Zinare” Ya Kore Surutan Tabarbarewar Tattalin Arzikin Kasar Sin
Gwamnati ta kuma yi kira da a lura kuma a sanya kare fararen hula ta hanyar ba da damar kula da jin kan dan Adam fiye da bukatar son kai.
“Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta damu matuka game da barkewar rikici tsakanin Isra’ila da Hamas da ya barke da sanyin safiyar Asabar 7 ga watan Oktoba, 2023 ta kuma yi kira da a tsagaita wuta.
“Gwamnatin ta yi kira ga bangarorin biyu da su yi hakuri, su ba da fifikon kare lafiyar fararen hula da kuma ba da damar kaddamar da ayyukan jin kai. Muna kira da a warware rikicin cikin lumana ta hanyar tattaunawa.” inji Ambasada Tuggar