A farkon makon nan ne kasar Falasdinu ta yanke shawarar dakatar da duk wata tuntuba, tarurruka da kuma daidaita harkokin tsaro da gwamnatin Isra’ila, domin nuna adawa da mummunan farmakin da aka kai a yammacin gabar kogin Jordan, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 8 tare da jikkata wasu 80.
An yanke wannan shawara ne a wani taron gaggawa na shugabannin Falasdinawa karkashin jagorancin shugaba Mahmoud Abbas a birnin Ramallah dake yammacin gabar kogin Jordan, kamar yadda wata sanarwa da aka fitar a hukumance ta bayyana.
- ‘Muna Cikin Fargabar Yiwuwar Ambaliyar Ruwa A Daminar Bana’
- Ina Son Kara Aure, Ko Me Yake Kawo Matsaloli Tsakanin Kishiyoyi Da Yadda Za A Magance?
Kamfanin dillancin labaran kasar Falasdinu WAFA ya ruwaito cewa, a yayin ganawar, Abbas ya yi kira ga Falasdinawa da su tsaya tsayin daka, da hada kai don kare kasa da mutuncinta. (Yahaya Babs).