Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya haramta duk wata zanga-zanga tare da kama duk wani dalibi da ke shirin tada zaune-tsaye a jihar.
Sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa n, ya sanar da matakin a ranar Laraba.
Gwamna Yusuf ya umarci ‘yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya da su kama tare da gurfanar da duk wanda ke da ke shirin yin zanga-zanga a jihar.
Wannan matakin na da nufin hana tada tarzoma a jihar.
Gwamnatin na zargin ’yan adawa na shirin yin amfani da kungiyoyin dalibai wajen tada zaune-tsaye, biyo bayan tsige Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.
Gwamnati ta haramta duk wata zanga-zanga a jihar, inda ta yi gargadin cewa za ta sa kafar wando daya da duk wanda aka kama.
Gwamnan ya gargadi kungiyoyin dalibai da su guji kawo rikici a Jihar Kano.
Gwamna Yusuf, ya bukaci ‘yan jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda suka saba, yayin da gwamnati ke kokarin wanzar da zaman lafiya.
Ya kuma jaddada cewa gwamnati na ci gaba da taka-tsan-tsan, kuma a shirye ta ke ta dakile duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya a Kano.