Rundunar ‘yansanda a Jihar Kano ta ce ta tura ƙarin jami’anta a fadar Sarki na 14/16, Muhammadu Sanusi ll da ke Ƙofar Kudu da kuma Gidan Nassarawa, inda Sarki na 15, Aminu Ado Bayero yake da zama tun bayan shigar da Sanusi ll fadar ta Kofar Kudu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar mai barin gado Usaini Gumel ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Litinin a birnin Kano.
- Gwamnatin Sakkwato Na Shirin Warware Rawanin Sarkin Musulmi – MURIC
- Kotu Ta Rushe Dokar Da Ta Tsige Aminu Ado Bayero A Matsayin Sarkin Kano
Gumel Ya ce sun ɗauki wannan matakin ne domin daƙile duk wata barazana da ka iya tasowa a waɗannan wurare biyu.
“Mun tura ƙarin jami’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya a Fadar Ƙofar Kudu, inda Sarki Muhammadu Sanusi ll yake da kuma ƙaramar fada ta Nassarawa, inda Sarki Aminu Ado Bayero yake da zama,” Cewar Gumel.
Kwamishinan bukaci mazauna birnin na Kano da su ci gaba da bai wa jami’an ‘yansanda haɗin kai ta hanyar ba su duk wani labari da zai tabbatar da tsaro a fadin jihar baki daya.